Sulhu : Yari Da Matawalle Sun Ɗinke Ɓarakar Da Ke Jamiyyar APC A Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
A yanzu haka jam’iyyar APC da ta nemi ta watse a jihar Zamfara, sakamakon jan daga tsakanin ɓangaren tshohon gwamna Abdulaziz Yari, da Sanata Kabiru Marafa, sun haɗe sakamakon sulhu da uwar jamiyyar ta masu. Wanda kuma wannan ya sanya yanzu haka suka haɗe da gwamna Bello Matawallen Maradun sun zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
Wannan ne ya sanya masu ruwa da tsaki a siyasar jihar Zamfara, da kuma masu muƙaman siyasa suke ta kai gaisuwar alfarma da godiya ga tsohon gwamna Abdulaziz Yari, akan haɗewa da sukayi da Gwamna Bello Matawalle
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara Ƙarƙashin jagorancin Tukur Umar Ɗanfulani ta kai ziyarar nuna goyon baya ga tsohon gwamna Abdulaziz Yari a gidansa da ke Talata-Mafara.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Ɗanfulani ya shaida wa Yari cewa shugabancin jam’iyyar a jihar ya yi matuƙar farin ciki da samun karɓuwar da ya yi masa ta irin wannan gagarumin tarba.
Ɗanfulani ya ce tun da ya zama shugaban jam’iyyar ya yi aiki tukuru tare da sauran ‘yan kwamitin ayyuka na jiha domin haɗa baki ɗaya a ƙarƙashin rufin asiri kamar yadda aka yi a shekarar 1999.
Haka kuma Ɗanfulani ya ƙara da cewa, a matsayinsa na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC a halin yanzu, ba za ta iya rabuwa da tsohon gwamnan wanda karamcinsa da ƙyaƙkyawar shugabanci da kuma kwarewarsa ta siyasa ce da ba za a iya wasa da ita a Zamfara ba.
Ya kuma buƙaci jiga-jigan jam’iyyar APC da su tabbatar da cewa haɗin kan da aka samu ya ɗore da kuma ƙara yawan ‘ya’yan jam’iyyar da suka shigo jam’iyyar musamman a yanzu da ƙasar nan ta kusa da zaɓe mai zuwa.
Shugaban ya ce, “Ina ba da tabbacin cewa zan ci gaba da bin gaskiya da adalci a cikin shugabancina inda ake yi wa dukkan mambobin kungiyar adalci”.
Jam’iyyar kuma za ta tabbatar da da’a da mutunta shugabanni a kowane mataki”. Daga karshe Ɗanfulani.
Da yake mayar da martani, tsohon gwamna, Abdulaziz Yari wanda ya nuna farin cikinsa da ziyarar ya godewa shugabannin da suka samu lokacin ziyartarsa.
Ya bayyana sulhun da aka yi a jam’iyyar APC a matsayin hanyar ci gaban Zamfara da jam’iyyar a dukkan matakai.
Yari ya godewa Allah bisa wannan ƙoƙari da sulhu da aka yi, inda ya buƙaci mabiya da su ci gaba da gudanar da wannan nasara ta hanyar jajircewa da saɗaukar da kai ga ci gaban jam’iyyar.
“Ina shawartar shugabannin jam’iyyar da su tsara dabarun yadda za su wayar da kan mutane game da muhimmancin yin aiki tare kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada”. Inji shi
Hakan zai tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa a ƙasar
Haka Yari ya bayyana fatansa na cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa jam’iyya ɗaya tilo da ta yi nasara a jihar Zamfara. Daga nan sai ya buƙaci waɗanda suka ji bacin rai sakamakon sulhun da su ɗauki hakan a matsayin wani aiki na Allah.
Kazalika ya yi kira ga ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar da su amince da sulhun cikin gaskiya da adalci, su kuma yi aikin ci gaba da ci gaban jihar.
