VC Na FUDMA Ya Yaba Wa Kungiyar Katsinawa Da Daurawa.
Mataimakin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsinma ya bayyana kafa kungiyar hadin kai ta Katsinawa da Daurawa a matsayin abunda ya dace saboda zai kawo ci gaba al’ummomin 2 ta fuska daban daban.
Armaya’u Hamisu Bichi, da ya samu wakilcin mataimakinshi Dr. Aminu Ado, ya sanar da hakan a lokacin da jami’an kungiyar suka kawo mashi ziyarar ban girma.
Ya ce jami’ar za ta bada dukkan goyan-baya da taimakon da kungiyar ke so don ganin ta cimma abubuwan da ta sanya gaba.
Ya bukaci membobin kungiyar da cewa su yi aiki tukuru don ciyar da hadin kai da zaman lafiya gaba a karamar hukumar Dutsinma.
Tunda farko, saida shugaban kungiyar hadin kan Katsinawa da Daurawan na karamar hukumar Dutsinma Sani Bawa Dutsinma ya ce sun zo ofishin mataimakin shugaban jami’ar ne don neman goyan-baya da hadin kansu.
