September 18, 2026

An Dage Dawowa Da Zirga Zirgar Jiragen Kasa Akan Hanyar Abuja Kaduna.

0

An dage dawowa da zirga zirgar jiragen kasa akan hanyar Abuja Kaduna a wannan Litinin din kamar yadda gwamnatin tarayya ta tsara.

Kamar yadda wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hannun daraktan sashen hulda da jama’a na hukumar Mahmud Yakubu ta bayyana, za a sake sanar da wata ranar a nan gaba.

Sanarwa ta kuma ce, za a dauki matakan tabbatar da ganin an sako wadanda aka yi garkuwa da su a harin da aka kai na ranar 28 ga watan Maris.

Ta shawarci iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da cewa su yi hakuri.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *