September 18, 2026

Kotu Ta Daure Tsohon Ma’aikacin Banki Shekaru 10.

0

Wata Kotun Majistare ta Jihar Legas da ke zama a Tinubu ta yanke wa wani tsohon ma’aikacin banki, Samuel Arayode, daurin shekaru 10 a gidan yari bisa samunsa da laifin sata da kuma aikata jabu.

Mai shara’a Adeola Olumide-Fusika, ta daure Arayode ne bayan ta same shi da laifuka uku da ake tuhumarsa da laifin satar N540,000 mallakin ma’aikacin sa da kuma yin jabun takardar shaidar kammala karatu ta kasa ta LASPOTECH da ke Lagos.

Alkali mai shari’a Olumide-Fusika ta yanke wa Arayode hukuncin watanni 18 a kan aikata laifin jabu, shekara bakwai kan laifuka biyu da laifin sata da kuma watanni 18 bisa laifin hada baki a kan laifuka uku.

Ta kuma umarci mai laifin da ya mayar wa bankin kudin da ya sata, tare da karawa da riba.

Kotun ta ce zai ci gaba da zaman gidan yari a lokaci guda, wanda ke nufin Arayode zai shafe tsawon shekaru bakwai ne kawai a gidan yari.

Hukuncin ya biyo bayan shari’ar da aka yi na tsawon shekaru bakwai a gaban alkalai biyu.

Jaridar LEADERSHIP ta ce, yan sandan sun shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya samu aikin ne a bankin Ikota, reshen Lagos ta hanyar amfani da satifiket na jabu a shekarar 2010.

Wanda aka yanke wa hukuncin, mai shekaru 28 a duniya, an ce ya aikata laifukan ne a shekarar 2014 yana dan shekara 20 a duniya.

An gurfanar da shi ne a kan tuhuma mai lamba L/125/2014 a ranar 26 ga Agusta, 2014, a gaban Babban alkalin kotun Majistare A.T. Omoyele.

Dan sanda mai shigar da kara, Ben Ekundayo ya shaida wa kotun cewa laifukan sun ci karo da sashe na 409, 285 (7) da 363 (1) na dokar laifuka ta jihar Lagos, na shekarar 2015.

Wanda ake tuhumar ya ki amsa laifinsa, inda bayan haka aka bayar da belinsa a kan kudi N200,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *