Zargin Batanci: Ana Zaman Dar-dar A Bauchi Yayinda Mutune 2 Suka Jikkata.
Ana ci gaba da zaman dar-dar da yiyyiwar barkewar doka da oda a karamar hukumar Warji ta jihar Bauchi sakamakon wani faifan bidiyo da wata mata Kirista ta wallafa a dandalin WhatsApp.
Jaridar LEADERSHIP ta samu labarin cewa, an yi zargin ta wallafa wani faifan bidiyo da ke dauke da kalaman batanci a cikin wani group na WhatsApp na abokan aikinta wadanda galibinsu Musulmi ne.
Rahotanni sun ce matar mai suna Misis Roda Jatau tana aiki da hukumar lafiya a matakin farko na jihar Bauchi.
“Matar ‘yar Gombe ce amma tayi aure a karamar hukumar Warji.”
“Ta buga wani faifan bidiyo na wani da ya bar Musulunci; A cikin faifan bidiyon, an ji mutumin yana zagin Manzon Allah, Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
“Kafin kiftawar ido, bidiyon ya fara yawo a shafukan sada zumunta kuma jijiyoyi sun fara tashi”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa jaridar LEADERSHIP.
Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun harbe wasu mutane biyu da suka yi yunkurin kona cocin ECWA a garin Warji biyo bayan faruwar lamarin wata majiya ta shaida wa wannan kafar yada labarai.
