September 19, 2026

Kotu Ta Ki Bada Belin Nnamdi Kanu.

0

Mai shari’a Binta Murtala Nyako ta wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ki amincewa da bukatar belin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, har sai an yanke hukunci kan zargin cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ta shirya a kansa.

Mai shari’a Nyako ta ce dole ne Kanu ya bayyana dalilin da ya sa ya karya belin da aka ba shi a baya, kafin ya samu abinda yake so daga kotun.

“Duk da haka, wanda ake tuhuma yana da ‘yancin sake shigar da bukatar,” Justice Nyako ya ce.

Kotun ta bayyana cewa tun a shekarar 2015 shari’ar Kanu ta ke fuskantar komabaya daban-daban saboda bukatu 19 da aka shigar a kan karar.

Don haka, ta roki bangarorin da su ba da damar a ci gaba da shari’ar don a iya tantance laifin.

Kanu dai ya shigar da karar ne a cikin takardar bukatar da ya gabatar bisa ga sashe na 6(6) da 36(5) da (6) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 da aka yi wa kwaskwarima, da kuma sashe na 161, 162, 163 da 165 na hukumar shari’a ta ACJA. , 2015, inda ya roki kotu da ta sake shi a matsayin beli, har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan tuhumar da ake masa.

Hakazalika ya roki kotu da ta umarci hukumar DSS ta gabatar da rahoton lafiyar wanda ake kara wanda a halin yanzu ke hannun ta.

A cewar jaridar LEADERSHIP, Kanu ya shaidawa kotun cewa, an gana masa azaba mai tsanani na tsawon kwanaki takwas a kasar Kenya, kafin daga bisani a mayar da shi gida Najeriya domin ci gaba da shari’ar sa.

Ya yi zargin cewa, yanayin lafiyarsa ya tabarbare, biyo bayan “wani abu mai guba” da ya ce an yi masa allurar da shi, wanda ya ce yana haifar da ciwon ciki da kuma bugun zuciya.

Ya jajirce cewa, hukumar DSS ba ta da kayan kula da lafiyarsa, Kanu ya shaida wa kotun cewa kuma an tsare shi ne a gidan yari, inda ya yi zargin cewa a kullum kwalwarshi na azabtuwa.

Shugaban na IPOB ya shaida wa kotun cewa, yana da masu tsayayye marsh i a bada shi beli bisa gaskiya, inda ya yi alkawarin cewa ba zai aikata wani laifi ba yayin da yake kan beli.

Baya ga haka, Kanu ya ce babu wata kotun Najeriya da ta yi masa shari’a ko kuma ta yanke masa hukunci, yana mai cewa yana da damar a bayar da belinsa.

Ya kuma ja hankalin kotun cewa, a baya an sake shi ne bisa dalilin rashin lafiya.

Sai dai gwamnatin tarayya ta bukaci kotun da ta ki amincewa da bukatar neman belin, inda ta dage kan cewa, Kanu ya fahimci girman shari’ar da ake yi masa, zai gudu daga kasar nan, ba zai kai kansa gaban kotun ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *