Sojoji Sun Kama Sojan Dake Siyarwa Yan Bindiga Alburusai A Zamfara.
Rundunar sojin Najeriya ta kama wani sojanta da alburusai 1,000 da ya yi niyyar sayar wa ‘yan ta’adda a kan Naira miliyan daya.
Sojan wanda ke aiki da sansanin ‘Forward Operations Base (FOB)’ da ke Galadi, karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, an kama shi ne da laifin sayar da alburusai da kayan soja ga ‘yan bindiga a jihar.
A cewar jaridar LEADERSHIP ta yanar gizo, sojojin hukunta sojoji ne suka kama sojan mai suna Bala Nura (19NA/78/3870) a jiya Laraba.
An kuma kama shi da harsashi guda 1,000 da ya yi alkawarin sayar wa ‘yan bindigar kan Naira miliyan daya.
Sojan a cewar majiyoyin ya amsa cewa ya sayar wa yan ta’addan zagaye 100 na alburusan akan kudi N100,000.
