September 17, 2026

Matukiyar Jirgin Sama Da Wasu Mutane 11 Sun Mutu.

0

Wata mata mai tukin jirgin sama a Najeriya, Adzuayi Ewuga, ta mutu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a tsakiyar kasar Kamaru.

Marigayiyar dai ita ce diya ta biyu ga Sanata Solomon Ewuga, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa kuma tsohon karamin minista a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce matukiyar jirgin ta mutu ne tare da wasu mutane 11 a cikin wani karamin jirgin sama mallakin kamfanin Caverton Aviation Cameron, lokacin da ma’aikatan jirgin suka rasa hanyar sadarwa, lamarin da ya yi sanadin hatsarin jirgin.

Jaridar LEADERSHIP ta ce, Kafofin yada labaran kasar Kamaru sun rawaito cewa jirgin ya taso ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na Yaounde Nsimalen zuwa Belabo da ke gabashin kasar, inda ya yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar dukkan mutanen da ke cikinsa.

Kamfanin Caverton Aviation Kamaru wani reshen ne na kamfanin Caverton Offshore Support Group da ke Legas a Najeriya, wanda ke da jirage masu saukar angulu na kamfanin Caverton Helicopters.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *