September 17, 2026

Ziyarar Masarautar Aisa Ga Sarkin Daura Ta Jihar Yobe

0

Daga Ibraheem El-Tafseer

A ranar Talata da ta gabata ne 3/04/2022 Sarkin Aisa, Alhaji Iliya Abdullahi Ibn Mayinta ya tara al’ummar masarautarsa domin kai ziyarar sada zumunci da Barka da Sallah ga mai martaba Sarkin Daura. Masarautar Daura, tana ɗaya daga cikin tsoffin masarautu masu tarihi a jihar Yobe da Borno.

Masarautar Daura tana cikin ƙaramar hukumar Fune da ke jihar Yobe a yanzu haka. Kuma ita ce ta haifi masarautar Aisa dake ƙaramar hukumar Fika da ke cikin jihar Yobe.

Tawagar Sarkin Aisa ɗin, ta isa fadar Sarkin Daura da misalin ƙarfe 11:00 na safe, bayan addu’o’i, sai Ɗan Masanin Aisa, Malam Babangida Ahmad ya bayyana maƙasudin ziyarar.

Ya fara ne da ayyana dangantakar da ke tsakanin masarautar Aisa da Masarautar Daura. Sannan ya kawo taƙaitaccen tarihin masarautar Aisa ɗin da kuma bayyana jerin jama’ar da suke riƙe da masarautun gargajiya na Aisa ɗin.

A nasa jawabin, Sarkin Daura, ya nuna jin daɗi matuƙa da ziyarar, ya kawo taƙaitaccen tarihin masarautar ta Daura, inda ya nuna cewa masarautar Aisa tushenta shi ne Daura. Wanda ya kafa garin Aisa daga nan garin ya tashi ya tafi can. Inji shi

Sarkin Daura, ya ɗauko tarihin al’ummar Daura tun daga tushensu na asali. Yace su asali mutanen Yemen ne, daga suka iso Nijeriya sai suka sauka a jihar Borno, suka warwatsu har zuwa nan (Daura) suka kafa wannan gari.

Masarautar Daura ta fi shekaru 800 da kafuwa, tana da tsoffin kayan tarihi waɗanda babu su a kaf faɗin jihar Yobe da Borno, sai dai a fadar Shehun Borno.

Hatta masarautar Lafiyar Bare-Bari dake jihar Nasarawa da Masarautar Misau dake jihar Bauchi, duk tushensu nan ne (Daura). Sarkin ya shiga da wakilinmu gidan ajiye kayan tarihi na masarautar, inda ya nuna masa kayayyakin tarihi masu yawan gaske da abubuwan al’ajabi.

Ya nuna masa wani jibgegen Tambari, wanda ya shafe fiye da shekaru 700 da wasu kujeru na Sarakunan da suka gabata a masarautar. Akwai gine-gine masu tsayi da kauri, waɗanda sun shafe shekaru sama da 400.

Sannan akwai ganuwar garin wanda waɗansu duwatsu na al’ajabi suka kewaye garin da sauran kayayyakin tarihi da daman gaske.
Sarkin Daura na yanzu, shi ne Sarki na 47 a jerin Sarakunan masarautar.

Sarkin ya bayyana alaƙar da ke tsakanin masarautar Aisa da Masarautar Daura. Yace mutumin garin nan (Daura), mai suna Aisami, shi ne ya tashi ya je ya kafa garin Aisa, don haka mutanen Aisa, da mutanen Daura duk tushensu ɗaya.

Sannan Sarkin Daura ɗin ya ɗauki sarautar gargajiya ta JARMA GANA ya ba wa Sarkin Aisa, Alhaji Iliya Abdullahi.

Sai Sarkin Daura ɗin ya yi godiya ta musamman ga marigayi Alhaji Ahmadu Kukuwale, wanda shi ne ya assasa wannan zumunci na Masarautar Aisa da Masarautar Daura, don haka ba za mu manta da shi ba. Inji shi

Masarautar Daura tana da manyan ‘yan Boko, ɗaya daga cikinsu akwai tsohon shugaban Jami’ar Maiduguri (vice chancellor), Farfesa Mala Muhammad Daura. Sannan shi ne shugaban Jami’ar Jihar Yobe na yanzu.

ABIN DA YA SA MUKA ƘIRƘIRI ƘUNGIYAR CI GABAN AL’UMMAR AISA

Ɗan Masanin Aisa, Malam Babangida Ahmad ya bayyana dalilin da yasa suka ƙirƙiri ƙungiyar ci gaban al’ummar Aisa (Aisa Community Development Association).

Garin Aisa, gari ne mai tarihi, wanda ya taɓa kafuwa a shekaru masu yawa a baya. Garin Aisa ya tara mutane masu yawa, wani dalili ne ya faru, wanda ya yi sanadiyyar watsewar garin gabaɗaya.

Amma daga baya kakanninmu suka dawo suka sake kafa garin. Mutanen Aisa, sun watsu a garuruwa da dama a faɗin jihohin Yobe da Bauchi.

Don haka shi ne muka kafa wannan ƙungiya don haɗa kan al’ummar Aisa a ko ina suke, da ciyar da garin Aisa da Masarautar Aisa gaba. Inji Ɗan Masanin Aisa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *