Jiki Magayi: Idan An Ga Dama A Bar Buhari Ya Yi Ta Mulki – Sule Lamiɗo
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo ya yi shaguɓe dangane da halin da ƙasa ke ciki na matsalar tsaro inda ya ce “ƴan Najeriya idan sun ga dama su bar Buhari ya tabbata a mulki har abada.”
Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana hakan ne a yayin wata hira ta musamman da ya yi da gidan Rediyon BBC Hausa a birnin tarayya Abuja.
Tsohon gwamnan ya kuma ce “jam’iyyar APC annoba ce a Najeriya, ta kawo masifa marar iyaka, gyaran barnar APC nan gaba aiki ne babba, tun da yake ta kawo gaba tsakanin ɗa da uwa, da tsakanin wa da ƙani da tsakanin gari da gari, dangi da dangi, addini da addini da kudu da arewa.”
“Amma duk inda ake son mu bayar da gudunmowa za mu bayar wallahi,” a cewarsa.
Sule Lamido ya ce saboda kaunar Buhari da ƴan Najeriya suka so ya yi mulki “an ce mana arna, an ce mana kirista, an ce ba ma son Musulunci, ba ma son arewa, komai an yi, an ma ce mu da ƴaƴanmu ɓarayi ne.
“An ce Buhari waliyyi ne, ma’asumi ne, kaza-kaza duk an yi, an ɓata mu.”
Ya ce “idan dai har yanzu ƴan Najeriya ba su dawo rakiyar APC ba to sai su tabbatar da Buhari ya yi ta mulki har abada.”
“Tun da suna ganin ya kyauta, to duk mu taru mu ce Buhari don Allah ya ci gaba da mulki har abada.”
Jigon na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya yi zargin cewa APC mai mulki ta rusa dukkan ginshiƙan da aka gina ƙasar a kai don tabbatar da haɓakarta.
A cewarsa, hakan ta sa PDP ta duƙufa don ganin ta karɓe mulki da kuma sake lale da nufin ceto Najeriya.
