Bikin Bashir Maishadda: Abubuwa 4 Da Suka Ɗauki Hankulan Jama’a
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Bikin babban furodusa a masana’antar Kannywood Abubakar Bashir Maishadda ya tara jama’a daga ko’ina cikin Najeriya harda wasu daga ƙasashen ƙetare.
Ana iya cewa biki ne da aka yi na kece raini da nuna isa kuma na shiga tsara da kuma nuna kara wanda ‘yan fim sun kafa tarihi babba a wannan kasaitaccen biki.
To sai dai kuma, bayan kammala bikin cikin nasara da kwanciyar hankali da taya juna murna ta nasarar da aka samu, hakan bai hana wannan biki barin baya da kura ba.
Idan za a yi nazari game da yadda wannan shagulgulan biki suka wakana alal haƙƙiƙa akwai abubuwa da dama da za a iya gani ta fuskoki da yawa, sai dai a wannan rubutu zan maida hankali akan wasu abubuwa guda hudu da jamaa suka fi tofa albarkacin bakinsu akan su.
- Abu na farko shine kowa yasan yadda shugaba kuma jagoran sabuwar kungiyar 13X13 Dauda Kahutu Rarara yake da sabon ango Abubakar Bashir Maishadda, mai gida ne gare shi kuma abokin sana’a.
To amma jama’a da dama musamman a kafar sadarwa ta zamani wato soshiyal midiya sun fi maida hankali akan wani hoto da aka ɗauki da Rarara da Bashir Maishadda da kuma amarya Hassana.
Salo da yanayin da aka ɗauki wanann hoto ya tada kura so sai, domin yanzu har sunan shugaban 13X13 ya canza daga ubangidan ango ko abokin sana’a yana neman komawa besty wannan hoto shi ke yawo a wanann kafa ta soshiyal midiya cikin hotunan bikin da aka ɗauka fiye da dubu goma.
To sai dai tambayar da ake yi shi ne, a ina wannan al’amari ya ta so, muna iya cewa ‘yan sa ido ne suka yi wa hoton mummunar fahimta shi yasa suke dangantashi da besty ɗin amarya bayan a zahiri kowa yasan ba haka ba ne.
- Abu na biyu da ya ɗauki hankali a wannan biki shi ne yadda A’isha Humaira ta zama kamar babu ita a wanann biki kasancewar bayyanar wasu hotona wanda aka ɗauka ita da sabon ango domin wani dalili na daban sun bayyana sati biyu kafin wannan aure.
Mafiyawa jama’a sun tafi akan cewa A’isha Humaira ita ce sabuwar amaryar Maishadda, kuma sun sa ido su ga irin rawar da A’isha Humaira zata taka, ta sarara a wannan biki na ubangidanta, amma sai aka nemeta a wasu hotonan kaura wanbai aka rasa, ko me ya faru oho!
Ganin dacewar aure tsakanin A’isha Humaira da Bashir Maishadda ya jawo cece ku ce da fatan alheri lokacin da waɗancan hotonan suka bayyana a soshiyal midiya, inda aka yi tunanin ita ce zai angwance da ita, shi kuma da yake dila ne sarkin dibara, sai ya yi wuf ya bayyana fuskarsa ta gaskiya tare da katin ɗaurin auransa da sahibarsa Hassana.
- Abu na uku shi ne, wanda za iya cewa ya zama abin tsoro ba abin mamaki ba, saboda an ce duniya ba tabbas kuma in yau kaine gobe ba kaine ba.
Yadda Adam A. Zango ya zama kamar sabon shiga a masana’antar Kannywood a wajan bikin babban furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya isa kowa yin la’asar saboda duniya ba tabbas.
Abinda yasa na ce haka shi ne ko shekara ɗaya ba a yi ba Adam A. Zango ya fito ya shaidawa duniya cewa shi ne Bahaushen da ya fi kowa shahara da suna a duniya da kuma masoya, lokacin yana jin ba kowa sai shi.
Ke duniya! me yasa zaki yi masa haka? Ga alama baya ɗaukar darasi daga na gaba da shi, Zango ya yi abinda yake a wannan harka, kila shi yasa ya fara ganin abinda baya so.
Hatta manyan shaddodi da aka kece raini da su a wajan wannan biki sai dai ka riƙa ganin hotonansa sun yi anko da mai shigar ‘yan daba nan wato Abale kuma ba kowa tare da shi, daman an ce hali zanen dutse…
Kwana huɗu aka yi ana wanann shagalin biki kuma duk da Adam A. Zango aka shi, amma kamar baya wurin, duniya ke nan!, ya gama ji da kai da nuna izzar ya faɗo ƙasa ba nauyi, yanzu jama’a ba ta shi suke ba, shi kan shi angon da ba fitowa yake a fim ba ya fi Zango farin jini a wannan gaɓar.
- Abu na hudu wanda shi ne ya zama abin tattaunawa a tsakanin al’umma shi ne irin kuɗaɗen da aka gani an yi wa amarya da ango liki da su a wajan wannan kasaitaccen biki, abubuwa da yawa suka zo a tunanin al’umma.
Na farko shi ne ina dokar da baban bankin Najeriya ya sanya ta hana yin likin kudi haka a bainar nasi? Sannan masu yin wannan liki suna yi domin bada gudummawar su ko kuwa da izza suka yi, ga dai Zango nan ya zama misali tun ba a yi nisa ba.
Haka kuma wannan liki da aka yi ya ƙara tona asirin masu shirya finafinai da ba su so ace basa taimakawa’ yan uwansu idan wata matsala ta faru sun sun kai gargara.
Sannan kuma ba sa son ana faɗin cewa sun yi watsi da ‘yan uwansu da dai sauran batutuwa da suka kewaye wannan kasaitaccen biki.
Anan muke cewa Allah ya ba ango da amarya zaman lafiya da ƙaruwar arziki ya cida ‘yan baya waɗanda har yanzu ba su shige ba, irin su Abubakar Sadiq Zazzaɓi da dai sauransu.
