‘Yan Sanda A Katsina Sun Samun Nasarar Kwato Shanu 149 Da Tumakai 33 A Hannun ‘Yan Bindiga.
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina.
Rundunar’yan sanda a jihar Katsina ta ce ta samu nasarar kwace shanu 149 da tumakai 33 tare da raunata wasu daga cikin ‘yan bindiga a Katsina.
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya shaidawa manema labarai haka a Katsina a lokacin da yake kwalemar masu laifi daban-daban a gaba ‘yan jarida.
SP Gambo Isah ya kara da cewa a ranar 22/02022 jami’an su na sirri suka samu rahotan cewa ‘yan bindiga sun kutsa kai a garin Kurami na karamar hukumar Bakori dauke da makamai masu hadarin gaske inda suka tafi da dabbobi da ba a san yawansu ba.
Ya ce da jin wannan rahoto sai jami’an ‘yan sanda da na sojoji da ‘yan banga suka datse hanyar da suka bi donin shiga cikin daji akan hanyar Sheme zuwa ƙanƙara.
“gamayyar jami’an tsaron mu sun yi nasarar tushe wannan hanya da ‘yan ta’ada suka biyo, ta garin Ƙwaƙware da ke cikin gundumar sheme cikin karamar hukumar Faskari inda suka bude masu wuta kan mai uwa da wabi, anan ne fa muka samu nasarar kwace shanu guda 149 da tumakai 33 bayan wasu daga cikin barayin dajin sun ranta ana kare.” In ji shi
A cewarsa da yawa daga cikin barayin dajin sun samu munanan raunuka da suka tsere da su cikin daji.
Haka kuma SP Gambo Isah ya bayyana cewa bincike akan al’amarin na cigaba da gudana.
