September 18, 2026

Kotu ta yi wa wasu matasa daurin talala sakamakon satar Turmin Daka A Kano

0

Kotun shari’ar muslinci mai zamanta a Ungogo karkashin jagorancin mai shari’a, Mansur Ibrahim Bello, ta hori wasu matasa 2 da daurin talala, sakamakon samun su da laifin sata da sayen kayan sata.

Kunshin zargin ya bayyana cewar, wanda a ke zargi na farko, Habibu Ibrahim, a na zargin shi da laifin sace turmin daka na mahaifiyar sa.

Yayin da Ammar Garba ake zargin shi da laifin sayan turmin sata.

Wakilin Radiyo Dala FM Kano Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, dukkanin su sun amsa laifinsu, kotun ta hore su da daurin talala na watanni shida.

Dala FM Kano

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *