Kungiyar Matasan Manoma Ta Karrama Alhaji Abubakar Musa Bamai
Kungiyar matasan Manoma ta kasa wato Young Farmers Network of Nigeria ta sha alwashin kawo gagarumin sauyi ta hanyar samar da sabbin tsare-tsare da za su bunkasa harkar noma a fadin kasarnan.
A yayin bikin karrama Alhaji Abubakar Musa Bamai da taya shi murna bisa mukamin da ya samu, shugaban gonar The Parisian dake Kano, Alhaji Mustapha Muhammad ya ce nadin ya zo a kan gaba kuma al’umma sun shaida hakan.
“Abin nan yazo gida, duk shekara ana tallafi sau uku, amma bamu taba ji ba. Wannan abin ya zo gida, bari mu nemi masu ruwa da tsaki mu gabatar dasu a wannan kungiyar.
Alhaji Mustapha Muhammad ya kara da cewa, babu Manomin da zai ce baya son tallafi.
“Babu manomin da zai ce baya son tallafi, wannan kyakkwan tsari ne da zai kai ga manoma.
“Idan ka kasa masu karbar tallafi da sunan manoma, kashi 50 ma ba Manoman bane. Wannan ya fito da tsarinsa da zai kai ga manoma na kasa”.
Shima anasa bangaren, Alhaji Musa Bamai wanda aka karrama ya lashi takobin ciyar da harkar noma gaba har ma da shigo da sabbin tsare-tsare domin tabbatar da cewa, Manoma sun amfana da tallafin kayan noma da suke bukata wajen samar da abinci da kasa ke bukata.
” Babu wata kafa da zai bada ayyuka da ake bukata kuma mutum ya yi dogaro da kansa kamar harkar noma. Mu samu mu nuna musu hanyoyin tallafi dasu samu su dogara da kansu.
“Har mata ba a barsu a baya ba, suma muna kokari mu sanyasu a wannan harka ta noma”.
Prime time Hausa
