September 17, 2026

Rikicin APC A Daura: Hon. El-Marzuq Ne Ya Kitsa Kama Hon. Shehu Abdu Daura. -Hon. Ibrahim Suleiman

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Al’ummar Karamar hukumar Daura na cikin alhini da bakin ciki bisa abinda suka kira tsabar zalunci da nuna isa da kwamishinan shari’a Hon. Ahmad El-Marzuq yake yi masu.

Shugaban tsaffin Kansiloli na karamar hukumar Daura Alhaji Ibrahim Suleiman ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina.

Hon. Ibrahim Suleiman ya cigaba da bayyanin cewa ‘yan sanda sun zo har gida suka kama wanda ya ci zaban fidda gwani a zaban Kananan Hukumomi mai zuwa Hon. Shehu Abdu Daura.

Ya ce wannan kamu da aka yi masa Babu wanda ya kitsa shi sai kwamishinan shari’a Hon El-Marzuq, saboda kayan da dan takararsa ya sha a zaban fidda gwani da aka gudanar a garin Daura a satin da ya gabata.

“Gaskiyar magana wannan Mutumin ya same annoba a wannan karamar hukuma da shugaban Kasa ya fito daga cikin ta, duba da irin abubuwan da yake saboda ya ga tashi ta kare a siyasa.” Inji Ibrahim Suleiman

Ya ce Hon El-Marzuq ya tsaida dan takara kuma sun fadi kasa warwas, inda ta kai sai da al’ummar Daura suka bada shaida ta hanyar zaban Shehu Abdu a matsayin wanda zai yi masu takara zaban da za a gudanar nan bada jimawa ba a karkashin tutar jamiyyar APC.

Kuma abinda yasa na ce Hon El-Marzuq shine kanwa uwar gami wajan kama wannan dan takara na mu shi ne, ya fito ya nuna cewa baya tare da mu, sanan hatta korafin da aka rubutu zuwa wajan ‘yan sanda daga wajan aka kawo shi” ya bada tabbaci

Hon. Ibrahim Suleiman ya ce dalilin da suka bada na kama Hon. Shehu Abdu shi ne, sun yi amfani da wasu yara a mazabunmu na waje, suka bada wani tallafi domin aci abincin da kama wajan kwana shi ne, daga baya aka gayyaci wadanda yara aka aka yi rubutu cewa wai wadanda yara suna min Hon. Shehu kudi.

Haka kuma ya cigaba da cewa, sai aka maida maganar cewa wai ya amshi kudin yaran ne da zummar sai sa ma musu aikin gwamnati, saboda haka wannan ba gaskiya bane, domin yaran sun tabbatar da cewa ba a yi haka da su ba.

Sannan acewarsa cikin yara hudu da ‘yan sanda suka gayyata domin bada shaida sun tabbatar da cewa ba ayi haka da su ba, sun bashi kudi ne a matsayin gudunmawa ba wai da ya sama musu aiki ba.

Haka ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na Daura da su kwantar da hankalinsu gaskiya zata yi halinta, saboda babu wanda ya isa ya karkatar da wannan nasara ta su.

Ya kuma bayyana halin da shi Hon. Shehu Abdu yake ci bayan ‘yan sanda sun gabatar da shi a gaban kotu, inda ya ce Hon. Shehun yana cikin wani hali, saboda haka sai ma likitoci sun yi aiki akan sa, saboda yana fama da ciwon asma da kuma ulsa.

Daga karshe ya yi kira da babbar murya ga gwamna Aminu Bello Masari da cewa suna bukatar adalci a wannan rigima da Hon. El-Marzuq ya asasa wajan lalata siyasar garin wanda yake gari ne na shugaban kasa da kuma ita kanta uwar jam’iyyar APC a matakin kasa da kuma jiha.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *