‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban ASUU Da Mutun 6 A Zamfara
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan shugaban kungiyar malaman jami’o’i t aASUU na jami’ar tarayya ta garin Gusau (FUGUS), Abdurrahman Adamu.
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da mutane shida a harin da aka kai gidan na shugaban kungiyar ta ASUU da ke Damba Quarters, a wajen Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Wani ma’aikaci a jami’ar kuma makusancin shugaban ASUU ya shaidawa majiyar DCLHausa ta gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Ada ne da sanyin safiyar Laraba inda su yi awon gaba da mutane biyar a gidansa.
majiya: DCL Hausa
