Karamar Hukumar Dandume Ta Raba Kayan Tallafi Na Miliyoyin Nairori A Katsina
Daga wakilinmu
Ƙaramar hukumar Dandume ta raba kayan gini na miliyoyin nairori ga mutanen da hareharen ƴan ta’adda ya rutsa da su a yankin. An kuma bada tallafin naira miliyan 1 ga mutanen.
Shugaban mulkin ƙaramar hukumar Ahmad Idris Mashi ya bayyana cewa an bada tallafin ne haɗin gwiwa da gwamnatin jahar Katsina.
Kamar yadda ya bayyana, an raba kayan ne ga al’ummomin Unguwar Rimi da Bango waɗanda ayyukan ƴan ta’adda ya rutsa da su a yankin.
Alhaji Ahmad Idris Mashi wanda ya yi jaje ga mutanen, ya buƙace su da su dage yin addu’a don ganin Allah ya kawar da wannan bala’in.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin kuma wakilin hakimin Dandume Mai Unguwa Musa ya bayyana talllafin a matsayin wanda ya zo kan kari
