Zamu horad da karin matasa sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani, Pantami
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace za’a horad da karin matasan Najeriya sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani.
The Nation ta rahoto cewa wannan na ɗaya daga cikin amfanar da yan Najeriya za su yi da hadin guiwar ma’aikatar sadarwa da kamfanin Huawei Technologies Nigeria.
Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin ɓangarorin biyu, da nufin ƙara inganta ilimin zamani (Digital Literacy) ga yan Najeriya.
Pantami yace: “Yarjejeniyar da FG ta sa wa hannu ta ma’aikatar sadarwa, a ɗaya hannun kuma kamfanin Huawei Nigeria, zai maida hankali ne wajen kara inganta kwarewar yan Najeriya.”
“Musamman sabida yadda duniya ke canza wa a yanzu, akwai bukatar dalibai su samu kwarewar fasaha da za su iya yin abu a aikace . “Shiyasa mukai tunanin samar da MoU domin ganin, a ɓangaren kokarin da kamfanin Huawei ke yi, sun tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan.”
A shirye mukule mu tallafawa Najeriya Shugaban Huawei Najeriya, Liuyan Trevor, ya bayyana cewa a shirye suke su taimaka wajen daga tattalin arzikin zamani a Najeriya ta hanyar ilimantar da matasan Najeriya su kware a bangaren fasaha.
Ya kara da cewa za su yi iyakar bakin kokarin su wajen gina duniyar fasaha ta hanyar inganta sashin tattalin arzikin zamani, kamar yadda
Daily Nigerian ta rahoto.
