September 17, 2026

Gwamnatin Anambra Ta Hana Sanya Ƙananan Siket A Matsayin Kayan Makaranta.

0

Gwamnatin jihar Anambra ta haramta sanya dan-tohi (mini skirt) a matsayin kayan makaranta a dukkan makarantun jihar, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.

Kwamishiniyar Ilimi, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ta bayyana hakan a garin Awka yau Lahadi, inda ta ce sanarwar dakatarwar ta zama wajibi ganin cewa makarantu za su koma karatu ranar Litinin.

Ta ce an sanar da dakatarwar ne ga sakatarorin ilimi na makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

Kwamishinar ta yi Allah-wadai da yadda ake samun karuwar sanya kananan kaya a matsayin kayan makaranta, sannan ta ce hakan ba daidai ba ne kuma ba za a amince da shi ba ga yara masu zuwa makaranta.

Ta ce, “ya kamata ɗalibi ya yi shiga ta birgewa kuma wadda ya kamata.”

“Tsarin kayan makarantar da aka yarda da shi a cikin jihar ana bukatar ya kai daidai gwiwa, ba irin kayan makarantar da ake ganin ɗalibai na sanyawa cen sama ɗangale ba a makarantu,” in ji ta.

Kwamishinar ta ce an hori sakatarorin Ilimi su tabbatar da cewa makarantu sun bi umarnin don ceto makomar daliban jihar.

Chuma-Udeh ta kuma bukaci sakatarorin ilimin da su sanya wa dalibai kyawawan dabi’u da tarbiyya ta yadda za su kasance masu tarbiyya da kuma hazaka.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *