September 17, 2026

Sana’ar Kanikanci Tana Iya Maida Mutum Biloniya – Sani Dogo Bakanike

0

Daga El-Zaharadeen Umar

Fasihin matashin Bakanike nan kuma ɗan na gada Bishir Sani Dogo ya bayyana yadda sana’ar Kanikanci take da rufin asiri fiye da kowane irin sana’ar ta hannu a wannan lokaci

Bishir wanda yake Ɗa ne ga marigayi Alhaji Sani Dogo wanda kafin rasuwarsa ya riƙe shugaban kungiyar Kanikawa ta jihar Katsina ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake hira ta musamman da kafafen yaɗa labarai a Katsina.

Matashin ya ce, da matasa sun san sirri da rufin asirin da ke cikin sana’ar gyaran mota lallai da ba su yi wasa da ita ba, ya ce duk da haka lokaci bai kore masu ba suna da sauran dama

“A wannan lokacin sana’ar Kanikanci ba zata hana ka yin karatu ba, domin mun yi karatun boko bakin gwargwado kuma mun yi na addini sannan ga sana’ar muna yi, ita ce cin mu da shan mu da kuma sutura.” Inji shi

A cewar sa mutane da dama sun zama miloniyas da wannan sana’ar musamman wadanda suka san ƙimarta da kuma darajarta, ya ƙara da cewa yanzu lokaci ne da ababan hawa suka yi yawa a cikin al’umma saboda haks Mota ce abokiyar rayuwar mutane.

Bishir Sani Dogo ya yi kira ga matasa da su guji bangar siyasa su rungumi sana’o’in hannu musamman gyaran mota akwai alheri mai yawa acikin sa ta yadda kullum bawa ba zai rasa abinda zai kai bakin salati ba.

“Ina ƙara shaidawa matasa duk wani Bakanike mai arziki ne, ko dai arzikin kuɗi, ko na jama’a ko na sanin malamar aiki, ya ce mutum mai irin wannan fikira ya wuce wasa a cikin al’umma.

Haka kuma Bishir Sani Dogo ya ce baban abinda yake alfahari da shi akan wannan sana’a ta Kanikanci shi ne yadda shima yanzu ya yaye wasu sun kafa kansu tare da yaran su suna cin abinci, ya ce idan har ya tuna wannan sai ya ji sana’ar Kanikanci ta gama masa komi a duniya.

Yace yana ganin mamakin matasan da suka tsaye kai da fata cewa sai gwamnati ta ba su aiki don taƙamar sun yi karatu, a maimakon su kana wata sana’ar ko da ta gyaran mota ce, ya ƙara da cewa wannan sana’a ta su har gyaran tarbiyya tana yi, tunda bata barin aiki banza ko zaman kwashe wando.

Daga karshe ya nuna bukatar da ke akwai musamman ga matasa da su rungumi wannan sana’a domin tsira da mutuncin su da na iyalansu a wannan rayuwa da babu tabbas a cikin ta.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *