September 17, 2026

An Bada Kyauta Ga Ɗalibin Da Ya Zana Kwamishinan Ilimin Jihar Katsina.

0

Daraktan samar da ingantaccen ilimi na ma’aikatar ilimi dake shiyyar Katsina ya ce kungiyoyin tsaffin dalibai, da masu hannu da shuni, da kuma kungiyoyin da bana Gwamnati ba nada muhimmiyar rawar da za su iya takawa don farfaɗo da ɓangaren ilimi.

Ahmed Abubakar ya fa fai hakan ne a lokacin da tsohon ɗalibin makarantar KCK Adamu Abdullahi Banye ke miƙa kyauta ga wani ɗilibin makarantar sakandaren KCK daya gudana a ofishin principal.

Kamar yadda ya bayyana, ya zama dole a haɗa hannuwa wurin ɗaya don ganin an ceci ilimi.

A tsokacinshi, faransifal ɗin makarantar Rabe Mudi ya buƙaci sauran tsaffin ɗalibai da su kwaikwayi wannan aikin don ƙarfafa ma ɗaliba gwiwa su ƙara ƙwazo.

Ya kuma yaba ma gudunmawar da kwamishinan ilimi Badamasi Lawal Charanchi ke bayarwa wurin ciyar da ilimin jihar nan ta Katsina gaba.

Mataimakin principal ɗin Musa Ali Tudun Wada ya yi nuni da cewa, bada kyautar ƙarfafa ma ɗalibai gwiwa ne su maida ma karantunsu hankali.

Shima da yake magana, principal ɗin makarantar Government Pilot Secondary School Mani Lawal Aliyu Muhammad ya shawarci iyaye da su ƙarfafa ma ƴaƴansu gwiwa don ganin sun maida ma koyan sana’o’i hankali.

Da yake magana tunda farko kuma wanda ke miƙa kyautar Abdullahi Adamu Banye ya ce zanen photon Kwamishinan ilimi da ɗalibin da aka ba kyautar mai suna Ahmed Kabir Umar ya yi ya birge shi.

An dai ba Ahmed Kabir Umar kyautar shadda yadi 10 da naira ₦5,000, haka kuma an ba mahaifiyyarshi kyautar turmin atamfa 1 da kuma shadda ga babanshi.

Kuma daga karshe mahaifiyar ɗalibin Binta Lamis Masanawa ta miƙa sakon godiyarta.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *