‘Yan Fim Mata Ku Tona Asirin Daraktoci Da Furodusoshi Da Suka Jefa ku Cikin Karuwanci
Tsokaci Daga Jamilu Aliyu BK
Duk da cewa ban dauki masu sana’ar Film wasu kamilallin mutane ba (saboda kwararan hujjojin da nike da su, na cewa da yawan su yan iska ne, kuma fasikai)
Kuma nasan cewa wanda ma basu harkan Film din akwai na banza da na kirki, kamar yadda a Film industry din ma akwai na banza dana kirki, wannan trending issue da Ladin Chima ta tado, kuma Nazeeru Sarkin Waqa ya kambama.
Wata babbar dama ce ga matan dake cikin wannan sana’ar, ya kamata su tashi, su farka, su zama courageous, su tona asirin directors and producers da suke saka su karuwanci, wanda yayi kama da sex slavery.
Bawai Kannywood or Nollywood ba, har a Hollywood akwai irin wannan scandals din. Abun rainin hankali ne, ace wasu taurarin sun fito suna ƙaryata wa.
Tun sadda ake yin Films masu daraja ma, mun san jarumai (mata) suna biyan kudi ko su bada jikin su kafin a basu movie roles.
Kowa ya sani, kannywood tana daga cikin shirmammun Films industries a duniya da zaka zama tauraro amma baka da komai da zaka gwada.
Ni a ganina, Wa’annan jarumai especially Mata, da ake cutar wa, ya kamata su cire tsoro da kunya suyi abunda ya kamata.
Ta riga ta ɓaci, ko sun tona wa kansu asiri ko not, munsan yawan cin su karuwai ne, wasu kuma sex slaves.
