September 18, 2026

An ƙaddamar da aikin Gina Ajujuwa Guda Tara Na Agile A Musawa

0

Daga Wakilinmu

A jiya talata ne, mai girma magajin Karachi Alhaji Abdullahi Yahya ya ƙaddamar da aikin da hukumar Agile suka gabatar a GDSS Musawa.

Wannan hukuma ta Agile, bankin duniya da haɗin gwiwa na gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Katsina ne ke tafiyar da shi.

Abubuwan da aka ƙaddamar sun hada:
Ajujuwa guda 9 babban dakin jarabawa(Hall) banɗakuna 2 Sashin mulki na makarantar tankin ruwa da zai Rarraba ruwan zuwa banɗakuna tare da kayan aiki (stationary) da dai sauran su.

Membobin kwamiti na SBMC dabsuka halarci taron ƙaddamar da wannan muhimmin aiki da suna yawan gaske

Daga cikin su akwai shugaban SBMC Abdullahi Yahya shugaban makarantar s baban bangare Abdu Hamisu da kuma shugaban ƙaramar sakandare Mal. Rilwanu Usman wanda baban mai gudanarwa akan harkokin mulki Malam Safiyanu Ibrahim Musawa ya wakilta tare Malam Mustapha Haruna Yau baban mai gudanarwa a bangare koyarwada sauran su.

Anyi taro lafiya an gama lafiya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *