September 17, 2026

‘Yan Sanda Sun Jikkata A Wani Hari Da Aka Kai A Sashen Binciken Manyan Laifuka Na Yan Sandan Jihar Abia.

0

Kimanin ‘yan sanda uku ne suka samu raunuka bayan da wasu ‘yan bindiga a daren Laraba, suka kai hari a sashen binciken manyan laifuka na yan sandan jihar Abia, hedkwatar ‘yan sandan Najeriya da ke kan titin Uzuakoli.

Majiyar Popular News Hausa ta Vanguard ta ce, Har yanzu dai ba a da cikakken bayani a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto, amma wata majiya ta ce an jikkata ‘yan sandan 3.

An ce an garzaya da wadanda abin ya shafa asibiti domin yi musu magani.

Akwai kuma fargabar cewa maharan sun kai hari a dakin ajiyar makamai, amma kokarin tabbatar da harin bai yi nasara ba saboda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Geoffrey Ogbonna bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Ko a shekarar da ta gabata dai wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene sun
mamaye wurin, inda suka kona wani bangare na ginin bayan sun sako fursunonin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *