September 18, 2026

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tabbatar Da Ariwoola A Matsayin Babban Jojin Kasa.

0

Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da Mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin kasa.

Tabbatar da Ariwoola a matsayin babban jojin kasa ya biyo bayan amsa tambayoyin da sanatoci suka yi masa da misalin karfe 12:45 na rana, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.

Idan za a iya tunawa, majalisar dattawa a ranar 26 ga watan Yuli, 2022 ta samu takarda daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke neman a tantance tare da tabbatar da mai shari’a Olukayade Ariwoola wanda da yake rike da mukamin babban jojin Najeriya domin ya zama cikakken jojin kasar.

Shugaban Majalisar Dattawan Ahmad Lawan, ya karanta takardar mai dauke da kwanan watan 25 ga Yuli, 2022.

Wasikar ta kasance kamar haka, “Bisa ga sashe na 231 (1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), na gabatar da nadin da majalisar dattawa ta yi ma Mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya.

Nadin Justice Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya da shugaba Buhari yayi, ta biyo bayan murabus din da tsohon babban jojin kasa Muhammad Tanko yayi a ranar 27 ga watan Yuni, 2022.

Murabus din Tanko dai ya biyo bayan zanga-zangar da wasu alkalai 14 suka yi kan batutuwan da suka shafi rashin samun abubuwan walwala.

Sai dai kuma, tsohon babban jojin, a cikin takardar murabus dinshi, ya bayar da dalilan batun kiwon lafiya a matsayin dalilin yanke hukuncin.

Idan za a iya tunawa, a watan da ya gabata ne shugaba Buhari ya ɗora Ariwoola a matsayin mukaddashin babban jojin Najeriya sakamakon murabus din da mai shari’a Ibrahim Tanko ya yi a kan batun rashin lafiya.

Bayan amincewar da majalisar dattawa ta yi, Ariwoola ya zama mutum na uku da ya rike kujerar shari’ar kasar karkashin gwamnatin Buhari.

Idan za ku iya tunawa, Mai Shari’a Walter Onnoghen shi ma ya taba zama babban jojin Najeriya karkashin gwamnatin Shugaba Buhari kafin ya yi murabus daga mukaminsa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *