September 17, 2026

2023: Yanzu Ya Kamata Arewa Ta Maidawa Bola Tinubu Biki. Cewar Sanata Ibrahim

0

Wani jigo a jam’iyyar APC daga jihar Katsina, Sanata Abu Ibrahim ya ce shekarar 2023 lokaci ne da arewa za ta biya ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya riƙa baiwa ‘yan takara da suka fita daga arewa a baya.

Sanata Ibrahim ya bayyana haka ne yau a Katsina yayin ziyarar da ya kai ofishin yakin neman zaben ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Katsina.

Ya tuna yadda Tinubu ya goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar lokacin da ya yi takarar kujerar ƙarƙashin rusasshiyar jam’iyyar ACN da kuma yadda ya goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya lashe zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Sanata Ibrahim ya tabbatar da cewa Tinubu shi ne mai kaunar arewa, inda ya ƙara da cewa duk “lokacin da aka zaɓi Tinubu tabbas zai bunƙasa muradin arewa”.

Jigo a jam’iyyar APC na Katsina ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa idan aka zaɓi Bila Ahmad Tinubu zai yi fiye da kyakkyawan aikin da ya yi a Legas don dawo da martabar Najeriya baki ɗaya.

Kazalika, Sanata Abu Ibrahim ya buƙaci al’ummar jihar Katsina da su zaɓi ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umar Raɗɗa.

Ya ce “Dikko matashi ne mai hankali da zai ciyar da jihar gaba idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar Katsina”.

Ya ƙara da cewa a yanzu ya koma Katsina ya jagoranci sulhu da kuma tallata takarar Tinubu da Dikko.

Sanata Abu Ibrahim Ya bayyana cewa a halin yanzu yana zagaye a jihar don tabbatar da cewa Tinubu da Dikko sun yi nasara a lokacin zaɓen da ke tafe.

A jawabinsa, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Katsina, Dakta. Dikko Radda ya gode wa Sanata Abu Ibrahim a bisa jagoranci irin na uba.

Ya tabbatar da cewa Sanata Abu Ibrahim a matsayin babban ginshikin yakin neman zaɓen Tinubu ba zai ɓata ran kowa ba a jihar Katsina a lokacin zaɓe ba.

Shima da yake jawabi mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa ya bayyana cewa Sanata ya zo ne domin a tabbatar da tabbatar nasarar Tinubu da Dikko.

Ya jaddada cewa jam’iyyar APC jihar Katsina babbar uwa ce mai tarin iyalai, mai hadin kai, inda ya ƙara da cewa “mu uwa ɗaya ne, uba ɗaya, babu ɓaraka a jam’iyyar”.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *