September 17, 2026

An Yi Kira Ga Kungiyar Yan Achaba Ta Magance Ce-ce-ku-ce Wajen Amsar Kudin Haraji.

0

Fasinjoji da sauran masu amfani da hanya suka yi wannan kiran a lokacin da muke zantawa da su.

Kiran dai biyo bayan la’akari da yadda ake ɗauki-ba-daɗi tsakanin jami’an kungiyar da ke amsar kudin harajin da kuma masu baburan da ake amsar kudin hannunsu.

Sannan masu amfani da hanya sun koka kan yadda ake cunkushe wasu daga cikin hanyoyin birnin Katsina a lokacin da jami’an kungiyar yan achaba ke kokarin amsar kudin harajin.

Daga ɓangaren masu babura kuma sun ce, suna nuna wannan turjiya ne saboda basu cin gajiyar kudin harajin da ake amsa hannunsu.

Saidai a jawabin shugaban kungiyar masu haya da baburan na Najeriya reshen na ƙaramar hukumar Katsina ya ce masu baburan ne basu goya masu baya wajen ganin an amshi kudin harajin cikin ruwan sanya.

Amma a cewarshi, “muna ɗaukar jami’an da suka cancanta, tare da basu horo domin amsar kudin haraji cikin ruwan sanyi.”

Kamar yadda ya bayyana, idan dan achaba nada gaskiya kuma ya cika sharudda mi zai hana shi tsayawa idan jami’an kungiyar suka tsaida shi akan hanya domin amsar kudin hajari.

Kabir Salisu Sani ya ce dama dukkan wuraren da ake amsar kudin haraji sai an yi fama da mutane suke biyanshi.

Ya ce dukkan dan achabar da ya yi rijista da kungiyar tana kare mashi lafiya, da lafiyar fasinjoji, da kuma taimaka mashi idan bukatar hakan ta taso.

Kabir Salisu Sani ya ce kungiyar na ba ƴaƴanta masu rijista kayan gyaran babura, taimaka ma waɗanda suka yi haɗari, dadai sauransu.

Dangane da maganar kudin haraji kau, shugaban kungiyar ya ce harajin da ake amsa na bangarori biyu: ƙarama hukumar Katsina da kuma kungiyar yan baburan hayar.

Daga karshe dai ya yi kira ga yan achaba su riƙa yin rijista da kungiyar, su goya ma kungiyar baya, su zama masu bin doka da oda don cimma abubuwan da kungiyar ta sanya gaba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *