‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 A Anambra.
Sojoji 5 ne da wani farar hula ɗaya suka mutu a wannan Larabar a Umunze da ke karamar hukumar Orumba ta Kudu a jihar Anambra yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude musu wuta.
Mutanen da lamarin ya rutsa da su suna cikin mota kirar Toyota Sienna ne yayin da ‘yan bindigar da ke boye kusa da wani banki a garin suka bude musu wuta.
Wata majiya a garin ta shaida wa majiyar Popular News Hausa ta Vanguard cewa, an shiga ruɗani a yankin bayanda yan ta’addan su ka yi harbe-harbe a wuri da ya mutane gudu domin tsira da rayukansu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, bai iya bayyana adadin wadanda suka mutu ba.
“An yi harbe-harben ne a kusa da bankin Zenith da ke Umunze, amma ba a samu cikakken bayani ba,” in ji mai magana da yawun rundunar yan sandan.
A cewarsa, rundunar ta baza jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a yankin, ya kuma kara da cewa dole ne a gurfanar da wadanda ke da hannu a harin.
Sai dai wata majiya da ta shaida lamarin ta ce: “ta ce har bankuna da shaguna saida suka rufe nan take, yayin da masu ababen hawa sukai ta juyawa baya.
“ Yan bindigar dai sun yi wa sojojin ne kwanton bauna a kan hanyar ta Umunze zuwa Umunneochi.
“Babu wanda ya ga alamar ‘yan bindigar kafin su fara harbin.
“Wasu daga cikin mu da ke kusa da bankin sun gudu don ceton rayukan mu. ’Yan bindigar sun mami sojojin ne ba tare da saninsu ba, dalilin da ya sa suka iya kashe su.”
