Kotu Ta Ki Sauraron Buƙatar Gwamnatin Najeriya Ta Janye Yajin Aikin ASUU.
ABUJA – Kotun masana’antu ta kasa da ke zamanta a Abuja a wannan Juma’ar, ta ki sauraron bukatar da gwamnatin tarayya ta shigar ta ba kungiyar ASUU umarnin gaggauta dakatar da yajin aikin da suke yi.
Kotun, a hukuncin da mai shari’a Polycarp Hamman, ta yanke, ta ki sauraron bukatar ne bayan da ta saurari lauyoyin da ke kare kungiyar da ke yajin aikin Femi Falana, SAN.
Majiyar jaridar Popular news Hausa ta jaridar Vanguard ta ce, Lauyan da ke kare gwamnatin Najeriya James Igwe, a ci gaba da zaman shari’ar na wannan Juma’ar, ya yi yunkurin shawo kan kotun ta saurari karar da suka shigar na neman a dauki mataki kan kungiyar ASUU.
Ya shaida wa kotun cewa lamarin ba na gaggawa ba ne, amma yana da amfani ga kasa domin miliyoyin dalibai suna gida tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar.
“Sashe na 47 na dokar rigingimun kasuwanci ya ba shugaba ikon ba da umarnin cewa, babu wani ma’aikaci da zai ci gaba da zama cikin yajin aiki a daidai lokacin da aka mika bukata gaban kotu,” in ji shi.
Ya kuma bukaci kotun da ta umarci kungiyar ASUU ta koma bakin aiki har sai an yanke hukunci.
Sai dai lauyan kungiyar ASUU Falana, SAN, ya ki amincewa da bukatar farko mai cewa, an shigar da karar ne don ci gaba da sauraronta.
Ya kara da cewa tun da an fara sauraron karar, ba a iya sauraron bukatar gwamnatin tarayya na bada irin wannan umarnin.
Baya ga haka, Falana SAN, ya shaida wa kotun cewa wadanda ya ke karewa na ci gaba da kokarin ganawa da masu ruwa da tsaki, ciki har da ‘yan majalisar wakilan Najeriya a ranar 20 ga watan Satumbar wannan shekarar domin lalubo hanyar da za a bi don warware matsalolin.
Falana ya kara da cewa, “Za mu yi bakin kokarinmu don ganin an warware wannan lamari, kuma muna rokon ɗayan bangaren da ya shigar da karar ya hada hannu da mu.”
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Hamman, ya tabbatar ma kungiyar ASUU cewa ba za a iya shigar da bukatar gwamnatin tarayya ba a wannan mataki na shari’ar ba.
“Wannan batu na nan gaba ne, ba a iya sauraronshi yanzu,” Kamar yadda alkalin kotun ya yanke hukunci.
Saidai ya bayyana cewa, za a fara sauraron bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar ne a zama na gaba.
A nasa bangaren, lauya mai kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa Ebun-Olu Adegboruwa, SAN, ya ja hankalin kotun kan bukatar da bangaren da yake karewa ya shigar na a saka shi cikin lamarin a matsayin mai sha’awar hakan.
Adegboruwa, SAN ya ci gaba da cewa, bangaren da yake karewa ya nemi a shigar da kara domin tilastawa gwamnatin tarayyar Najeriya mutunta yarjejeniyar da ta kulla da malaman jami’o’in da ke yajin aiki tun a shekarar 2009 don tabbatar da adalci.
Ya bayyana cewa daya daga cikin abinda SERAP ke nema daga kotun shi ne, umarnin ko kotun za ta iya shigar da su cikin karar.
Bayan ya saurari bangarorin, mai shari’a Hamman ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Litinin.
Hakazalika, kotun ta kuma dage karar da kungiyar dalibai ta kasa NANS ta shigar da ASUU da ma’aikatar ilimi ta tarayya bayan an karanta ta.
Ko da yake Debo Ikuesan, wanda ya bayyana a madadin shugaban kungiyar dalibai Umar Lawal, ya bukaci a bayyana ranar da za a ci gaba da sauraren karar, amma Mai shari’a Hamman ya umarce shi da ya shigar da kara kafin ranar Talata mai zuwa kan ko kotun kula da masana’antun na da hurumin sauraren karar.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar ne kungiyar ASUU ta fara yajin aikin na makonni hudu.
Daga nan kuma ta tsawaita yajin aikin har abada, a ranar 29 ga watan Agusta, biyo bayan rugujewar tattaunawar da aka yi tsakanin malaman jami’o’i da gwamnatin tarayya.
Sai dai gwamnatin Najeriyar ta ce tana son kotu ta yanke hukunci kan yajin aikin ko kuma akasin haka.
Yayin da kungiyar ASUU ta zargi gwamnatin Najeriya da rashin cika alkawari a tattaunawar da su yi, gwamnatin ta hannun ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tunkari kotu domin tilasta wa malaman da ke yajin aikin komawa bakin aiki.
