Yajin Aikin ASUU: Kotu Ta Ɗage Sauraron Karar Da Aka Shigar.
Kotun masana’antu ta Najeriya ta sanya ranar 16 ga watan Satumba domin sauraren karar da gwamnatin tarayya ta shigar wadda ke kalubalantar yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ke yi.
A zaman da aka yi wannan Litinin ɗin, Lauyan da ke kare shirin SERAP Ebun-Olu Adegboruwa ya nemi a shigar da su cikin karar saboda bangaren da ya ke karewa nada irin wannan bukatar da ke neman kotu ta tilasta ma gwamnatin tarayyar Najeriya cika alkawullan da ke tsakaninta da malaman jami’o’in da ke yajin aikin a halin yanzu.
Sai dai lauyan gwamnatin tarayya, Tijjani Gazali ya soki matakin na SERAP saboda bai cika sharudda ba, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar AIT.LIVE.
Shi ma lauyan kungiyar ASUU Femi Falana a nasa bangaren ya yaba da kokarin lauyoyin da ke cikin karar.
Mai shari’a Peter Hamman a hukuncin da ya yanke, ya ce kotun ba ta kai ga sauraren karar da SERAP ta shigar ba, ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Satumba domin ci gaba, tare da bayyana cewa yana jagorantar shari’ar ne kawai a matsayin alkalin da ke kan kujerar a halin yanzu, amma za a tura karar zuwa wani alkali domin yanke hukunci.
A shari’ar wadda Ministan Kwadagon Najeriya Chris Ngige ya shigar, gwamnatin tarayya na neman a ba da umarni ga malaman jami’o’in da ke yajin aiki su koma bakin aiki kamar yadda sashe na 18 karamin sashe na 1b na dokar rikicin kasuwanci ya tanada na 2004 duba da cewa yajin aikin na kawo cikas ga ilimi na kasa.
