September 17, 2026

Galadiman Katsina Ya Umarci Masu Gari Su Kafa Kwamitocin Inganta Tsaro.

0

Galadiman Katsina hakimin Malumfashi ya umarci masu gari da su kafa kwamitocin inganta tsaro a yankin.

Mai Shara’a Sadiq Abdullahi Mahuta mai ritaya ya bada wannan umarnin ne lokacin taron tsaro daya gudana a dakin taro na karamar hukumar Malumfashi.

Ya yi kira da su bada gudunmawarsu duba da cewa tsaro aiki ne na kowa da kowa, inji Popular News Hausa.

A jawabin shugaban karamar hukumar Maharazu Adamu Dayi ya yi kira ga masu hannu da shuni da sauran al’umma da cewa su bada gudunmawar su ta la’akari da cewa gwamnati kadai bata iya magance matsalar tsaron da ake fama da ita.

Ya ce suna bukatar motocin sintiri 7, bindigu, rigunan ruwa, fitilu da kuma kudin alawus don badawa ga yan vigilante a yankin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *