An Kori Wani Dan Sanda Daga Aiki Saboda Amsar Na Goro.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sallami wani dan sanda mai suna Mr. Richard Gele dake da mukamin insefekta daga aiki bayanda aka kama shi a wani faifan bidiyo mai yawo yana amsar na goro daga hannun jama’a da a ranar 25 ga Yuli, 2022.
Insefektan mai lamba AP/No.188547, wanda har zuwa lokacin da aka kore shi, yana aiki da rundunar ‘yan sanda ta Mobile Force 77 Squadron, Okene, jihar Kogi, inda aka tura shi titin Itobe – Anyigba domin kare lafiyar masu amfani da hanya da masu ababen hawa, a kan hanyar, inda lamarin ya faru.
Korarren a insefektan wanda ya fito daga jihar Benue, an ɗauke shi aikin dan sanda ne a watan Satumba shekarar 2000 inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, CSP Muyiwa Adejobi ya fitar ta ce, “Korar tasa ta zo ne bayan bin tsarin ladabtarwa na cikin gida da aka same shi da laifin da ake tuhumarsa da shi daidai da wasu dokoki da suka shafi dabi’un ‘yan sanda.
Ya ce, ” don haka yanzu ba jam’in yan sanda bane.”
“An cire wa dan sandan kayan aiki kuma an mika shi ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kogi domin daukar matakin da ya dace.
“A lokacin da babban sufeton yan sandan Najeriya Usman Alkali yake bayyana jajircewar shi wajen inganta ayyukan yan sandan daidai da tsarin kasa da kasa, ya gargadi dukkan yan sanda da su nisanta kansu daga karbar na goro da saba doka.
“Ya bukace su da su nuna jajircewa da kishin kasa wajen gudanar da ayyukansu.”
