September 19, 2026

NNPP Ga Buhari: Ka Sanya Dokar Ta Ɓaci A Jahohi Biyar Na Arewacin Najeriya

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Baban jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Katsina ta yi kira ga shugaban ƙasa Muhammad Buhari da ya sanya dokar ta ɓaci a jihohi biyar na arewacin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.

Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Katsina Alhaji Sani Liti ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Katsina.

Jahohin da jam’iyyar NNPP ta yi kira a kafa dokar ta ɓaci sun haɗa da jihar Katsina da Zamfara da Kaduna da Neja da kuma Sakkwato.

Alhaji Sani Liti ya ƙara da cewa yanayin da waɗannan jihohi suke ciki na rashin tsaro ya kai in taha, saboda haka a duba lamarin domin cutar al’ummar da ke waɗannan Jahohi.

Shugaban jam’iyyar NNPP ya ƙara da cewa saka dokar na aƙalla watanni shida wanda hakan zai taimaka wajan baiwa gwamnatin tarayya damar ɗaukar sha’anin tsaro da mahimmancin gaske.

” Haka kuma muna kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa miliyan daya aikin sa kai sannan ta ba su horo na musamman domin tunkarar wannan matsala ta tsaro a wadannan jihohi masu fama da matsalar tsaro” in ji shi.

Haka kuma jam’iyyar NNPP ta ƙara da cewa yin haka zai ƙara ba gwamnatin tarayya damar kulli asusun ajiyar jihohin da aka ƙaƙaabawa dokar ta ɓaci domin yin amfani da kudaden jihohin wajan yin amfani da su a yaki matsalar tsaro.

Hon. Sani Liti Ya ce idan har gwamantin tarayya bata dauki wannan mataki ba. Suna kira da babar murya ga majalisun jihohin da aka yi kira a kafa dokar ta ɓaci akan su, da su fara gabatar da shirye shiryen tsige gwamnonin waɗannan jihohi

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *