September 19, 2026

Hukumar kidaya Ta Najeriya Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Manhajar Kidaya.

0

Hukumar kidaya ta Najeriya ta kaddamar da sabon tsarin manhaja da za a yi amfani da ita wurin aikin kidayar mutane da gidaje.

Da yake magana a Abuja, shugaban hukumar kidayar ta Najeriya Nasir Isah Kwara ya ce wannan manhaja za ta kasance mai sanya ido a lokacin aikin kidaya don ganin an inganta tattara bayanan mutane a fadin Najeriya, ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce manhajar za ta tabbatar da ganin an binciki bayanan mutanen da za a naɗa a lokacin aikin kidayar na shekarar baɗi.

Shugaban hukumar ya bayyana sabuwar manhajar a matsayin abunda zai taimaka wurin samar da sahihan bayanai domin gudanar da tsare tsaren kasa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *