Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa INEC Ta Ƙara Wa’adin Yin Rijistar Karin Zaɓe A Katsina
Hukumar zaɓe ta ƙasa reshen jihar Katsina na sanar jama’a cewa sun ƙara wa’adin yin rijista ga waɗanda shekarunsu ya kai goma sha takwas a duniya.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar reshen jihar Katsina Aliyu Garba Adosa ya shaidawa Popular News Hausa haka a Katsina.
Aliyu Garba wanda ya ce ada an shirya dakatar da yi wa ‘yan ƙasa da suka kai kimanin shekaru sha takwas rijista a ranar 30 ga watan Yuli 2022 a duk faɗin Najeriya.
“Yanzu za a cigaba da yin wannan rijista har illa Masha’Allahu, saboda haka muna kars kira ga waɗanda ba su yi ba kuma shekarunsu sun kai da su harzarta ofisoshin hukumar domin yin rijista” inji shi
Haka kuma ya ƙara da cewa akwai isassun ma’aikata da kayan aikin yin wannan rijista a dukkanin ofisoshin hukumar da ke faɗin jihar Katsina wanda aka samar domin jama’a.
Tuni dai Sarakuna da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki da kungiyoyi ke kira ga jama’a da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe wanda suka ce da shi mutum ke samun damar yin zaɓe sannan ya zaɓi wanda yake so.
