2023: Zamu Samar Da Sauyi A Ƙaramar Hukumar Dala Da Yardar Allah – Hon. Usman Anto
Daga Babangida Sunusi, Kano
A cigaba da zagaye da neman goyon bayan al’ummar ƙaramar hukumar Dala da ke jahar kano yasa ɗan takarar kujerar majalisar jiha a zauren majalisar dokokin jihar Kano Hon. Shu’aibu Anto yakai ziyara ga majalisar kansilolin mazaɓu goma sha biyu da ke akwai a Dala dan neman goyon bayan al’ummar da suke wakilta.
Hon. Shu’aibu Anto lokacin ziyarar yace babu abinda ya kawoshi wannan zaure daya wuce neman goyon bayan kansilolin mazaɓu goma sha biyu da ke akwai a ƙaramar hukumar Dala da samun nasarar cigaba da gudanar da ayyukan Alkhairi da inganta rayuwar jama’ar wannan ƙaramar hukuma ta Dala da ta ƙasa samu ga wancan da yake ci a yanzu.
Anto ya cigaba da cewa yasan babu yabo kuma bazai zama fallasa ba kan irin kokari da sukayi wajen inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar Dala a dan iya damar da suka samu na muƙami daya riƙe a baya dan duk wanda yake wannan zaure shaida ne.
Haka kuma yace a takarar da ɗan takararsu na Jam’iyar APC yayi ya samu nasara a matakin zaɓe na farko ya gudanar da ayyuka da dama da yanzu haka ake amfana da su kama daga asibit,i gyara magudanan ruwa da hanyoyi amma kuma yanzu haka baisan dakali guda daya da za’ace lawal hussaini yayi ƙaramar hukumar Dala ba.
Ɗan takarar kujerar majalisar jihar ya kuma ce da yawan al’umma suna cewa a halin yanzu ana yin mutum ne ba jam’iya ba bisa cancantarsa dan haka yake ƙara kira ga jama’ar wannan ƙaramar hukumar ta Dala da su ƙara fahimtar zaɓar wanda zai wankesu daga matsalar da take addabarsu ba ɗan cika tsereba.
Shima da yake yiwa wakilinmu ƙarin bayani bayan taro a madadin kansilolin kuma shugaban gamayyar kansilolin jihar kano kansila mai wakiltar mazaɓar Gobirawa a Dala Hon. Ibrahim Abubakar yace lallai wannan ɗan takarar ya cancanta ya jagoranci Dala.
Sannan ya buƙaci al’ummar ƙaramar hukumar Dala da su fito su marama Anto baya dan a ganinsa idan mutum ya cancanta ya jagoranci Dala to sune matakin gaba da zasu kawoahi kuma nagartarsa yasa suka zoma da jama’ar Dala shi dan zai taimaki jam’iyar APC da sauran mutanen da yake wakilta idan har ya samu dama a zaben da zaizo idan Allah ya kaimu shekarar 2023.
Daga karshe anyi maganganu da dama da suke nuni da cancantar wannan ɗan takara Hon. Shu’aibu Usman Anto dan sahale masa ya zama ɗan takarar da jam’iyar APC ya kamata ace ta barwa damar tsayawa takarar majalisar jiha da zai wakilci ƙaramar hukumar Dala ta jjhar Kano tare da yi masa fatan samun nasara.
