September 17, 2026

Muna Cigaba Da Kawo Sauyi Ta Fuskar Kasuwanci Da Taimakon Jama’a A jihar Kano – Albdulƙadir Alkamatu

0

Daga Babangida Sunusi, Kano

A ƙoƙarin sa na wayar da kan matasa da al’ummar jihar Kano dangane da mahimmancin dogaro da ta fuskar Kasuwanci da matakin da ya kamata ace al’umma sunbi wajen ganin zama masu dogaro kansu da kamfanin Alkamatu ke ta fafutukar yi ga al’ummar jihar Kano ya kara buƙatar neman sahilewar gwamnati da masu hannu da shuni kan ƙara zuwa ɗan zuba hannu jarinsu.

Alkamatu Abdulkadeer ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da bita karo na ɗaya da na biyu wajen ganin jama’a sun kara samun haske da fahimtar ta yaya zasu gudanar da kasuwa musamman waɗanda suke neman taimako daga gidaunyar Tony Elumelu da kamfanin Alkamatu Brain Box Solution ke ta fafutikar ganin kowa ya zama miloniya ta fuskar Kasuwanci a ji
har Kano.

Idan dai ana biye shugaban Kamfanin na Alkamatu yana gabatar da bitar ne a gidan Radio zamani da Premier FM a kowace ranar larabar kowane mako da yanzu an shiga mako na biyu wajen gabatar da shirin bitar Kasuwanci bama ga waɗanda suke nema ba a’a harma da wanda ba su cikin tafiyar sukan amfana da shirin ta karatun da shugaban da ke “feɗe biri harwutsiya ya yi bitar da zata ɗauki tsawon makonnitara kafin kammata.

Idan dai ba’a manta ba gidauniyar TEF ta samu damar baiwa matasa sama da ɗari da goma tallafin naira milyan biyu ga kowa a kwanan baya ƙarƙashin wannan kamfani na Alkamatu Brain Box Solution da suke ƙoƙarin ganin an samarma da matasa hanyar dogaro da kai ba dare ba rana a jihar Kano dama sauran jihohin arewa.

Haka kuma shugaban Kamfanin na Alkamatu ya buƙaci jama’ar da suke bibiyar wannan kamfani da su kara sa Kamfanin addu’ar da zata ƙara zama jigo da jagaba wajen ƙara samun nasara kamar yadda aka samu a baya.

Daga karshe yana miƙa godiya tare da fatan gwamnatin tarayya da mataki jihar Kano za su lura tare da la’akari da wannan tafiya ta su ta taimakon al’ummar ƙssa da jihar Kano da zuba nasu hannun jarin da sai ƙara fito da matasa daga kangin babu da zaman banza da wannan bawan Allah ya keyi da shi bama ɗan arewa kuma ba bahaushe ba, sannan shugaban Kamfanin ya kuma miƙa godiyarsa ga dukkan waɗanda suke taimakon wannan tafiya ta su a kowane lokaci.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *