September 18, 2026

Ina Da Tabbacin Zan Cinye Zaɓan Fidda Gwani Na Gwamna A jami’yyar APC -Mustapha Inuwa

0

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar APC a zaɓe mai zuwa Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya ƙara bada tabbacin cewa yana da ƙyakkyawar fatan cewa zan lashe zaɓan fidda gwani da zai gudana a ranar juma’a 20 ga watan Mayu, 2023

Dakta Mustapha Inuwa yana wannan bayani ne ga manema labarai a lokacin da yake amsa tambayoyi game da zaɓan fidda gwani da ke tafe na jam’iyyar APC.

Ya ce daga irin abubuwan da yake ji da kuma gani dangane da wannan zaɓe da fidda gwani yana da ƙwarin gwiwar lashe zaɓen fidda gwani da za a yi da yardar Allah.

“Ni ban ɗauka kuɗi na amfani ba wajan sayen Delegates ba domin haka ta faru a 2015 lokacin ba mu da gwamnati wasu ‘yan takara sun yi amfani da kuɗi amma ba a zaɓe su ba, saboda haka bana ganin cewa kudi suna da wani tasiri a zaɓen fidda gwani.” In ji shi

Haka kuma Dakta Mustapha Inuwa ya ƙara bada tabbacin cewa idan Allah ya ba wani ba shi ba, to za a taro a yi aiki tare domin samun nasarar jam’iyyar APC a jihar Katsina da kuma ƙasa baki ɗaya.

Dangane da batun sauya sheƙa da wasu kafafen yaɗa labarai na zamani ke yi cewa Dakta Mustapha Inuwa zai yi ya bada amsa da cewa bai ga dalilin yin haka ba, yana mai cewa koda ya bar PDP korarsa aka yi, aka daina yi da shi.

Ya kuma ƙara da cewa masu yaɗa hotansa da na tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso kuwa ba yanzu bane aka ɗauki wannan hoton ba, an ɗauki wannan hoto ne lokacin rasuwar mahaifiyar Alhaji Ɗahiru Mangal a Katsina.

“Bani da wani shiri koma wane iri na canza sheka Daga jam’iyyata ta APC zuwa NNPP saboda kawai an ga hotona da na tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso” in ji

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *