Har yanzu Jonathan bai zama membanmu ba — Bayelsa APC.
Shugaban jam’iyyar APC Dennis Otiotio, ya ce a hukumance har yanzu tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bai zama dan jam’iyyar APC a jihar ba.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar wayar tarho da jaridar PUNCH a yau Alhamis.
A cewarsa, Jonathan zai iya komawa APC ne kawai idan shugaban jam’iyyar na kasa, Adamu Abdullahi ya ba shi dama a hukumance.
Otiotio ya bayyana hakan ne a yayin da ake ta rade-radin cewa tsohon shugaban kasar ya koma jam’iyyar APC ne a unguwar Ogbia da ke Bayelsa.
Ya ce, “Ina ganin wanda ya kamata ku tambaya shi ne shugaban jam’iyyar na kasa. Shi ne zai ba shi (Jonathan) dama.
“Kawo yanzu bai shiga jam’iyyar mu a hukumance ba. Ka tambayi shugaban kasa ko ya ba shi dama.”
Shugaban jam’iyyar APCn na jihar, ya bayyana Jonathan a matsayin babban dattijo a jiha”.
Otiotio ya ce yana kyau idan Jonathan ya yanke shawarar komawa jam’iyya mai mulkin a hukumance.
