September 18, 2026

Kwamitin Yaki Da Shaye-Shaye Da Gyaran Tarbiyya Ya Damke Matasa 67 Da Kama Kwaya Ta miliyan 2 A Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar

Kwamitin Yaki Da Masu Shaye-Shayen miyagun kwayoyi da gyaran tarbiyyar tare da hana bangar siyasa ya yi gagarumar nasara a lokacin bukukuwan Sallah inda suka kama matasa 67 da kwaya da kuɗin ta ya kai naira miliyan 2.

Kwamitin dai yana ƙarƙashin mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro Ibrahim Katsina wanda kuma ASP Nasiru Lambu ke jagorantar jami’an tsaro domin yin aikin.

Da yake jawabin irin nasarorin da kwamitin ya samu Alhaji Ibrahim Katsina ya ce kauraye ba su ji da daɗi ba a lokacin bukukuwan Sallah, domin kuwa sun gamo da fushin Baradan Nasiru Lambu.

Ya ƙara da cewa an yi nasarar damke mutane 67 a lokacin bukukuwan Sallah da ke kokarin tada zaune tsaye, wanda ya ce ya zuwa yanzu tuni an shirya wani tsari da zai maida su turba madaidaiciya.

Mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro Ibrahim Katsina ya ce haɗin gwiwar jami’an tsaro sun yi nasarar kama kwaya da aka shirya kaiwa ‘yan ta’ada ita a cikin da ji.

” Wannan kwamiti ya samu nasarar kama wanda ƙwayoyi da suka haɗa da tremadol mai nauyin kilo 250 da kuɗin da ya kai naira miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai sai kuma Exol 5 da kuɗin da ya dubu ɗari biyu da casa’in da takwas kuma tuni an shirya kone su baki ɗaya” inji shi

Alhaji Ibrahim Katsina ya bayyana cewa matasan da aka kama ba wai za a kai su gaban kuliya ba ne, gwamnatin jihar Katsina ta yi haɗin gwiwa da Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi domin saita su da ɗora su hanya maƙabuliya.

Ya ƙara da cewa gwamnati zata ɗauki nauyin duk abinda za a yi wa kowane matashi har zuwa lokacin da aka lura ya samu kan shi ya dawo cikin hayyacinsa

A cewar sa wanann kwamiti zai cigaba da farautar ɓata gari a duk inda suke har sai jihar Katsina ta sai to al’amura sun dawo cikin hankali da lumana

Haka kuma baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro ya yabawa kokarin jami’an tsaro musamman Baradan Nasiru Lambu da suke dage wajan samun wannan nasara.

Popular News Hausa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *