Shuwagabannin Jami’yya Na Da Muhimmiyar Raya Da Za Su Taka wajan Cin Zaɓe – Hon. Sani Aliyu Ɗanlami
Dubun dubatar magoya bayan Hon. Sani Aliyu Ɗanlami sun yi dirar farin ɗango zuwa shalkwatar Jami’yyar APC ta ƙaramar hukumar Katsina domin neman albarka akan takarar da
Hon. Sani Aliyu zan yi ta ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya a zaɓen 2023.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ce baban dalilin da yasa ya kawo wannan ziyara a ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina shi ne neman albarka ga shugabannin jam’iyyar saboda mahimmancin su wajan ɗan takara.
Tun da farko da yake nashi jawabin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ce shuwagabannin jami’yya sune gishirin siyasa saboda haka suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajan samun nasarar kowane ɗan takara.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami wanda ake yi wa laƙabi da mai raba alheri ya yi bayanin cewa babu yadda za a samu nasara ba tare da haɗin kan shuwagabannin jami’yya ba, wanda hakan tasa ya zo domin ya nemi albarka tare da nuna masu fom ɗin takara da ya saya kuma yake son iyayen jami’yya su sanya masa albarka a matsayin sa na ɗa mai biyayya
“Duk da cewa shugaban jam’iyya baya da kuri’a to amma yana da mahimmancin gaske wajan zaɓan fidda gwani domin shi ne zai shiga lungu da sako wajan neman jama’a da za su marawa tafiyar ɗan takara koma wanene baya.” Inji shi
Ya ƙara da cewa wasu da cikin mahimman ayyuka da shugaban jam’iyya ke yi sun haɗa da duk lokacin da ka samu nasara shi ne zai bi jama’a rumfa-rumfa da gida-gida sannan ya tsare akwati duk domin a samu nasara, saboda a cewar Hon. Danlami shuwagabannin jami’yya dole a yi ma su biyayya.
Haka kuma mai neman takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya ya yi wa shuwagabannin jami’yyar wani albishir da cewa lallai gwamna Aminu Bello Masari ya jaddada cewa duk wani sha’anin da ya shafi jami’yya a ƙaramar hukumar Katsina to da su za a yi shi.
Sannan kuma Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya yi kira gare su da zo a yi wannan tafiya da ke da alamun nasara tare da su, saboda haka a haɗa kai baki ɗaya da sauran ‘yan takara domin kaiwa tudun mun tsira.
Hon. Sani Aliyu mai Raba alheri ya ce duk lokacin da ɗan takara ya samu nasara a zaɓen fidda gwani to daga wannan lokaci aiki ya koma wajan shuwagabannin jami’yya da kai kanka ɗan takara, wajan neman jama’a waɗanda aka yi takara da su da kuma sauran al’umma masu kaɗa kuri’a domin a samu nasarar da ake buƙata.
A cewar sa shuwagabannin jami’yya babu abinda suke so illa a ƙara masu ƙwarin gwiwa ta yadda za su gudanar da aikin su cikin nasara da jin daɗi.
Shima da yake nasa jawabin maraba ga dubun dubatar magoya bayan Hon da suka haɗa da kungiyoyi da ‘ yan kasuwa da ‘yan Boko da ‘yqn siyasa da ‘yan uwa da abokan arziki shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina Alhaji Ibrahim Saulawa ya ce yau dai kam sun yi baban bako a ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina.
Ya cigaba da cewa Mai Raba alheri Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya sayi Fom har ya cika ya zo ofishin jam’iyya domin neman tabaraki kuma insha’Allahu zai samu.
Ya ce Alhamdullahi yadda ka cika wannan fom na takarar ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya Allah ya baka sa’ar cinye zaɓe.
