September 18, 2026

Anyi Kira Ga Gwamna Bagudu Na Kebbi Da Ya Samar Da Motar Kashe Gobara A Argungu

0

Daga: Comrade Musa Garba Augie

Allah ya jarabci Makarantar Masarautar Argungu dake jihar Kebbi da Iftila’in gobara cikin daren nan, Argungu Emirates School.

Sakamakon rashin motar kashe gobara Fire Service wutar tayi sanadiyyar konewar makarantar, al’ummar Ƙaramar hukumar mulki ta Argungu sunaji suna gani wuta tanachi babu halin matsawa kusada ita saboda gudun ceton rayuwa.

Kaf kananan hukumomin dake jihar Kebbi babu wadda takama kafar Argungu girma da yawan jama’a amman abun bakin ciki shine babu motar kashe gobara Fire Service koda guda daya

Mai girma gwamnan jihar Kebbi Sen, Atiku Bagudu muna kira gareka dakayi gaggawar kawo muna agaji cikin garin Argungu

Daga karshe muna rokon Allah S.W.T daya kara karemu da dukkanin wasu masifu

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *