September 17, 2026

Dalilin Da Yasa Muka Haramta Ƙungiyar Sa Kai – Gwamnatin Jihar Katsina

0

Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin Jagoranchin Gwamna Aminu Bello Masari, ta Haramta Ayyukan Yan Sa Kai a fadin Jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Mai Ba Gwamna Shawara Akan Harkokin Tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina.

Kamar yadda takardar ta bayyana, tsayar da aikace-aikacen Yan Sa Kai din ya biyo bayan kashe-kashen mutane da ake yi ba gaira babu dalili a Jihar.

Takardar ta kara da cewar dokar ta fara aiki ne nan take daga yau Litinin 14 ga watan Fabrairu na wannan shekarar da muke ciki.

Takardar ta ce Gwamnatin Jihar Katsina ta aminta ne kawai da aikin yan Kungiyar Sintiri wanda suke a karkashin kulawar Yansanda da sauran Jami’an tsaro da masu rike da sarautu a Jihar.

A sabili da haka,daga yanzu Gwamnati ta bayar da umarni akan cewar duk wani da ake zargi da ayyukan ta’addanci da aka kama a hannanta shi ga jami’an tsaro domin daukar matakinda ya kamata.

The Fact 24

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *