September 18, 2026

Yadda Layin Man Fetur Ke Barazana Ga Tattalin Arzikin Jihar Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Tun da sanyi safiyar yau juma’a aka wayi gari a Katsina da manyan layukan man a mafiyawan gidajen man da ke cikin garin wanda haka ya jefa ayar tambaya da dama.

Wannan matsala ta fara sannu a hankali har take neman zama wani baban kalubale ga al’umma ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki na yau da kullin.

Haka kuma akwai zargi mai karfi da ke nuna cewa manyan dilalan man fetur suna boye shi saboda tunanin cewa zai kara kudi nan gaba, batun da Kamfanin man na NNPC ya ce baya da tushe balantana makama.

Wannan matsala dai ta shafi kowane bangare na rayuwa kama daga karin kudin ababan hawa da kuma kayan masarufi na yau da kullin wanda wannan matsala ta karancin man fetur ta shafa kai tsaye

Wadanda za su dandana kudar su game da wannan matsala shi ne talaka, saboda duk abinda aka debo akansa zai kare.

Hakan tasa wani lokaci Malamai ke jan hankali ga ‘yan Kasuwa da su rika duba halin da talakan Najeriya yake ciki kafin daukar kowane irin mataki na kasuwanci.

Ya zuwa yanzu dai garin Katsina ya dauki wani sabon yanayi na kunci da rashin man fetur ya haifar, inda zaka rika ganin dogayen layukan a gidajen man fetur.

Shin ko wane irin matakai Hukumomi ke dauka don ganin an kawo karshe wannan matsala? amsar da har yanzu ba a ji ba daga bakin mahukunta ba anan jihar Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *