September 18, 2026

An yi Kira Ga Gwamnatin Jihar Katsina Da Ta Duba Batun Saida Man Fetur acikin Galan

0

Daga Bello Salmanu Sayaya

A gaskiya ya kamata Gwamnatin jihar Katsina ta duba yiwuwar janye dokar nan ta hana sayarwa mutum man Petur a Galon a gidan mai duba da yadda a yanzu gidajen man da ke sayar da man sun yi karanci, ga halin rashin wadata da yayi wa akasarin mutane yawa, wanda ya sa ba kowa ke da sukunin sayen man mai yawa wanda zai dade masa ba.

Sai kaga mai ya qare ma mutum cikin abin hawan sa gashi nesa da gidan mai,gashi kuma babu damar ya dauki Galon yaje gidan mai a bashi mai saboda wannan dokar,kuma an hana ‘yan bunburutu masu sayarwa a gefen hanya.

Sai kaga mutum ya shiga wani hali ya rasa yadda zai yi da abin hawan sa,musamman mota.Nisan wani wurin bai yiwuwa a tura motar zuwa inda gidan mai yake,shi kuma ba abin ya bar motar a nan ba yi masa barna ko sata.

Haka ma masu Injunan markade da Generator,haka zaka mutum ya yo hayar motar nan Hi-jet ko Vespa mai taya 3 ta dauko masa Generator azo gidan mai ya sha mai.

Kuma dai duk dokokin nan da aka sanya saboda matakan tsaro akasari duk an janye su sai wannan ta sayar da mai a Galon,kuma dai matsalar rashin tsaron da kashe kashen jama’ar dai har yanzu ana fuskantar su duk da wannan dokar.

Masu ababe hawa da yawa suna fuskantar wannan matsalar karewar mai bagatatan nesa da gidan mai kuma su rasa yadda zasu yi.

Don haka don Allah ya kamata Gwamanati ta sake duba wannanan dokar a qalla a bada damar sayarwa mutum ko da Galon daya ne, ba Jarka ba.Allah Ya sa a duba kuma gyara.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *