September 18, 2026

Jam’iyyar APC Na Neman Yi Wa Mambobinta Kofar Raggo a Katsina

0

Wata sanarwa da aka fitar daga ofishin baban Darakta akan kafafen yada Labarai na zamani ga gwamnan jihar Katsina na cewa akwai wasu ka’idoji da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ya kamata su cika kafin shiga filin zaban fidda gwamni na MSU neman Takarar Kansila a karamar hukumar Katsina

Kwamitin shirya zabe na Karamar hukumar Katsina yana sanar da membobin APC baki daya cewa duk wanda zai je zaben kansiloli da zai gudana a yau lahadin 6/2/2022 ya tabbatar da yazo da sabon katin jam’iyyar APC da aka sabunta wato (Membership card) da kuma katin zabe na INEC ( voters card )

Bugu da kari, Sai wanda yazo da wadannan katittikan guda biyu kuma mutum ya tabbatar da katittkan da yazo da su na mazabar shi ne kana a bar mutum ya shiga filin zabe.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC a jihar Katsina ke tunkarar zaban Kananan Hukumomi a karon farko cikin shekaru shida.

Da fatan Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya amin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *