Masari Ya Kaddamar da Kotunan Sasanshi domin Rage Cinkoson Shari’a
Daga Abdulhadi Bawa, SSA Social Media
Duba da yadda tarin shari’u yayi ma kotuna yawa, wanda kuma mafi yawancin shari’un na rigingimu ne dake tasowa tsakanin al’umma daga cikin harkokin su na yau da kullum, wanda shiga tsakani, yin sulhu da sasanci na iya warware su, yasa babbar kotun jiha (High Court) tare da goyon bayan gwamnatin jiha ta yanke shawarar bude cibiyoyi na musamman domin warware irin wadannan matsalolin, maimakon a kai su kotu.
An bude irin wadannan cibiyoyi guda biyu a cikin garin Katsina, nasarorin kuma da suke samu wajen warware rigingimu, yin sulhu da sasanta al’umma yasa ci gaba da bude su a sauran sassan jihar nan ya zama wajibi.
A yau, Alhamis 3 ga watan Fabarairu 2022, Gwamna Aminu Bello Masari ya bude irin wannan cibiya a garin Malumfashi ya kuma bude wata a garin Funtua.
A jawaban da ya gabatar, Gwamnan yayi kira ga al’umma da mu rungumi wadannan cibiyoyi domin sulhu alkhairi ne. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jiha tayi wa dokar tsarin kananan hukumomi gyaran fuska domin kyautata tsaro.
A cikin wannan gyara da akayi, an kafa kwamitoci hawa ukku domin sa ido da daukar matakan da suka dace cikin al’amurran zamantakewar al’umma.
Wadannan kwamitoci anyi su a matakin Maiunguwa, Magaji da kuma Hakimi. Sun kuma kunshi Malamai, Dattawa, Shuwagabannin sana’o’i daban daban da ake yi sai kuma jami’an tsaro.
Ya kuma yi kira ga al’umma da kada mu gajiya wajen addu’o’in neman zaman lafiya da tsaro daga Allah Madaukakin Sarki.
Shi kau a nashi jawabin, Babban Jojin Jiha Maishari’a Musa Danladi Abubakar ya bayyana cewa mafi yawancin shari’un dake gaban kotuna an shigar dasu ne sakamakon rashin fahimta da kuma samun masu shiga tsakani nagartattu.
Hakan yasa suka nemi goyon bayan gwamnatin jiha domin wadannan cibiyoyi a karkashin masana shari’a domin saukaka ma kotuna.
Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu ya rufa ma Gwamnan baya wajen wannan aikin alkhairi, tare da rakiyar wasu manyan jami’an Gwamnatin Jiha.
