2023: Umar TATA Ya Kaddamar Da shuwagabanin A Matakin Kananan Hukumomin Katsina
Umar Abdullahi Tsauri (TATA) ya gudanar da taron kaddamar da shuwagabain a matakin kananan hukumomin da za su jagoranci tafiyarsa ta neman kujerarn gwamna jigar Katsina a shekarar 2023 A Katsaina.
Wannan taro ne wanda ya kumshi wakillai kadai na jiha, gunduma da kuma Kananun Hukumomi na jihar Katsina baki daya. Irin zaratan mutanen da aka zabo a cikin wannan tafiyar ke nuna nasara a fili, domin kuwa duk cikin wanda aka baiwa jagoranci a cikin wadannan al’umma babu wanda ba jajirtacce bane, babu wanda baida mutunci a inda ya fito.
Shugawabanin sun yi fatan cewa idan Allah ya tabbatar masu da Umar Tata a matsayin gwamnan jihar Katsina a shekara ta 2023, za a samu canji mai ma’ana saboda haka ne ma suka yi fatan Allah yasa alkhairi a cikin wannan tafiya, Allah ya kaisu lokacin da wannan bawan Allah zai kawo iri sauyi da alkhairin da ya saba a fadin jihar Katsina.
Shima a nashi sakon Umar Tata ya bayyana cewa zai yi biyayya ga inda zatayi amfani, wurin nema ba zai zama sakarai ba, kuma bai yarda duk mai tafiyarsa ya zama sakarai ba.
“Kujerar gwamna Allah ke badawa, duk inda ake neman alfarma masoyina ya nemamun alfarma inda bai iyawa ya kirani ni zanje in nemi alfarma, duk ranar da Allah yasa na zama gwamnan jihar Katsina bazan cima kowa mutunci ba kuma banda niyar cika kowa mutunci ba da yardar Allah!” inji shi
