Mutun Da Sana’arsa: Jan Hankalin Matasanmu Maza Da Mata
Game da muhimmancin yin sana’a kowace iri ce, in dai ba ta saba wa dokar Allah ba, ko ba ta saba ka’idojin da gwamnati ta kaf ba. Domin akwai sana’o’in da ba haramun ba ne a Addini, Sana’a ga matasa ta zama wajibi bisa la’akari da halin da ake ciki a duniyarmu ta yau.
Domin ba za a iya cewa gwamnati za ta iya sama wa kowane matashi aikin yi ba, ko da kuwa ya yi karatu zuwa na Digiri ne ko gaba da Digiri, ballantana kuma matasahin da bai samu halartar makaranta ba, Amma ya iya lekawa wanchen offishi zuwa wanchan ofis.
Ita sana’a tana da muhimmanci ko da kuwa a ce mutum ya yi karatun boko ne, domin zai iya zama bai samu aiki ba, ko kuma ya samu aikin, amma saboda halin da a ke ciki a yau, albashin da yake dauka ba ya iya biya masa bukatunsa na yau da kullum.
Ni Abdurrazaq Yahaya Ina Sana’a, inayin kwangila, Ina saye Ina saidawa, Ina wanki da Guda da sauran huddodi na kasuwanchi, Ina da Company wanda nayi ma Register da cooperate Affairs, ban tsaya kallon nayi boko ba har na Kai matakin digiri na biyu ba.
Yanzu abubuwa sun lalace ta yadda zaka ga wani matashin yana da Aure, wasu kuma su ke daukar nauyin iyayensu, sannan kuma ga hidindimun dangi da sauran al’ummar da ke tare da su, Amma baya Saida Fari Balle Baki, ya ta’allaka dukkanin nemansa wajen Roko, bara, maula da kai karar Ubangiji Mahaliccinmu wajen Abokan Halitta Wanda Hakan bai dace ba. Sau da yawa akan yi bayanin matasa, matasa, matasa, manyan gobe Wanda a zahiri ba na goben bane na tun jiya ne, yau da Kuma goben ga Wanda yasan chiwon kanshi.
Wannan ya zama wajibi ne bisa la’akari da cewa su matasan ne ginshikin duk wata rayuwa mai dorewa ta al’umma. Don haka idan Allah ya sa matasa suka gyaru, to dukkan al’umma ta gyaru. Saboda haka kuma babu wata hanya ta gyaruwar matashi kamar samun sana’ar dogaro da kai, ta hanyar dogaro da kai ne ake samun matashi natsattse wanda babu ruwansa da shiga duk wani tashin hankali ko aikin da bai dace ba.
Idan matashi yana sana’a, babu yadda za a yi a same shi wajen wasu ayyukan da ba su kamata ba, kamar dai yadda yake a fili cewa duk wani matsahin da aka samu a duk wata hayaniya, to idan aka bincika ba shi da wata takamaimiyar sana’ar da yake cin abinci a ciki, wanda hakan ne ma ke ingiza shi don gudanar da wadannan munanan ayyuka.
A matsayina na wakilin matasan karamar Hukumar katsina Ina kiran Yan uwana matasa da babbar murya akan su nemi Sana’a.
Tarihi yazo mana a dukkanin annabawan da Allah ya aiko babu wani Wanda baya da sana’ar da ya shahara a kanta, kowanansu Yana sana’arsa.
Allah ya ganar da matasanmu Amin
Alhamdulillah, Ina Taya Dan’uwa Comr Muhammad Zakariyya Kuma Aboki, murnar Sabon wurin Chi da Sha Mai suna #BANBOO_EATERY_SPOT da ya bude a No. 24 katuru road U/sarki Kaduna.
