Wata Kungiya Ta Karrama Masari, Inuwa Da Kanwan Katsina
Daga Wakilinmu
Wata ƙungiya da ba ta gwamnati ba ta karrama uwar gidan gwamnan jihar Katsina.
Sauran waɗanda ƙungiyar ta karrama sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad da Kanwan Katsina hakimin Ƙetare, Alhaji Usman Bello Kankara.
Ƙungiyar mai suna Ultimate Youth Development Association ta bada lambobin karramawar ne a cibiyar koyar da sana’o’i dake Filin Samji nan cikin garin Katsina.
Uwar gidan gwamnan Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari ta samu wakilcin sakatariyar yaɗa labarun ta Hauwa Ibrahim Jiƙamshi a lokacin taron.
Da ya ke magana a wurin taron, Kanwan Katsina hakimin Ƙetare Alhaji Usman Bello Kankara ya buƙaci masu hannu da shuni da su taimaka ma ƙungiyoyin fararen hula don ganin sun samu damar yi ma al’umma aiki a jahar Katsina.
Hakimin ya kuma yi nuna da cewa, ayyukan ƙungiyoyin da bana gwamnati ba na taimaka ma ƙoƙarin gwamnati wurin bunƙasa rayuwar al’umma.
Hakimin wanda ya samu wakilcin sarkin labarun shi Jamilu Hashim Gora, ya ce lambar karramawar za ta ƙarfafa masu gwiwa wurin taimaka ma al’umma.
Tunda farko, saida shugaban ƙungiyar Aminu Yusuf ya bayyana cewa, an kafa ƙungiyar ne don a taimaka ma marasa karfi a cikin al’umma.
